webnovel

TA ISO

A deadly virus was detected in rose city and kills people within seconds. The government issued a state of emergency until a cure is found. A handsome zillionaire volunteered to find the cure, in the process he met Asiya the gorgeous pharmacist who was stuck in her work place due to the government orders. Love builds between them as the virus kills and threatened to wipe out the entire city. However, the cure brought them closer and then........

Fatimazahra35 · perkotaan
Peringkat tidak cukup
20 Chs

BABI NA GOMA TOFA! SAFIYAN ANNOBA

Gadafi na cikin mota yana tuki yana jin sauti yana kada kai, hannushi daya kan stirring yana rawada yatsunshi, sigari a baki yana zukan abinshi yana busawa. Windon mota a sauke don hayakin ya fice. A hankali ya fara taka birki yana kallon gaba dashi cigari a baki, har motar ta tsaya. Wayanshi nata kara amma ina hankalinshi baya kan wayan.

Motocine ba adadi a cunkushe kaman lokaci daya suka yi hatsari, ya fito daga motarshi yana kallon mutanen cikin motocin babu mai motsi, a takaicema babu kowa a waje wurin tsit. Kirjin gadafi ya fara bugawa, yana takawa ya isa wurin motar dake kusadashi.

Lekawa keda wuya yaga mutanen ciki a langwabe, idanuwanshi suka zaro, sigarin ya fadi kasa, meke faruwane haka? Fittt wata mata ta wuceshi tana ihu annoban ta iso, can wasu maza da yara suka rugo suka wuceshi, saurayi ya juyo yayi mishi gargadin in yana son ranshi ya bar wurin kuma karya taba gawawwakin.

What! Gawa!! Sun mutune duka!!! Amma.....wani dattijo yazo ya fadi a gabanshi. Gadafi ya sankare yana kallonshi, ko motsi dattijon baiyiba. Ya mutu! to me ya kasheshi? Zuciyar gadafi ta bada dammm. Mutane sunkai ashirin suka shigo ta layin dayake, basu iso gareshiba sai a mace.

Zubewa sukeyi daya bayan daya har saida na karshen ya zube kusada motarda gadafi ke tsaye. Ji yayi kanshi yayi wani luuuu, ya fara jada baya. Wata karamar yarinya tazo taja hannunshi tana cewa yazo su gudu da tsamin bakinta, iyakarta shekara 4. Tuni ya sureta ya lafta a guje ya turata motarshi ya shige ya tada yabar wurin a sittin.

Duk inda yabi a rose city abu dayane yake gani, gawa. Yayita yawo har motarshi ta fara son mutuwa. Ya duba yaga fetur ya kare. Matsala, yanzu ina zai samu fetur a yanda gari ya hargitse haka? Motanta tsaya a wani unguwa wurin shiru. Gadafi ya bude mota zai fita sai yaji surutun yarinya ya waigo.

"Dani gida". Ya sankare, zata gida! ya akayi yarinya ta shigo motan!! Can ya tuna abinda ya faru hankalinshi ya dawo. Ashe shine ya surota ya taho da ita. Ta fara son yin kuka, tana kallonshi. "No no no, karki yi kuka, inane gidanku?"

"Ni gida". Yayi sauri ya zarota daga seat ya fita daga motan. Yana kalle kalle ya hango wani mutum yasa kyalle a fuskanshi tsaye jikin wani katon shago yanata kallonshi. Gadafi ya fara zuwa inda mutumin yake, ya kusa isa mutumin ya daga hannu ya dakatardashi. Cakkk gadafi ya tsaya yana kallonshi.

Mutumin ya lura da kayan da gadafi ke sanyeda tsaf suke, ya kalla yarinyar gashin kanta har gadon baya, kitson kanta ya tsufa, gashin yayi ja. Sanye take da gown pink amma da kayan da ita kanta yarinyan sun zama kalar kasa brown. Mutumin ya duba su da kyau yaga lafiyansu lau ba wanda ya fadi ya mutu.

"Daga ina kuke?"

"Motata mai ya kare, ina son in maida yarinyarnan ne gidansu, tazo min tace mu gudu, mutane nata mutuwa, Wai make faruwane!? A kidime yayita bada jawabi. Mutumin ya lura gadafi a rikice yake, ya mishi nuni ya karaso.

"Ka taba gawa ko inda gawa take?"

"Ya za ayi in taba gawa!"

"Muje" Mutumin ya juya ya fara tafiya zuwa shagon.

"Ina zamu?"

"Inda akwai kariya daga cutar dake kashe mutane". Gadafi na biye dashi daukeda yarinyar suka shiga shagon.

Anan yayita zama har kwana biyar. Ya taradda mutane sunkai goma sha a wurin. Suna fake suna jiran annoban ta lafa, sannan kowa yasan inda yayi. Anan ne mutumin mai suna zayyad ya mishi bayanin abindake faruwa a gari. Shagon akwai t.v, tanan gadafi ya kara ganin hasaran rayuwa da cutar ta kawo.

Yarinyar dake taredashi ta makale mishi duk inda zashi tana biye dashi, yaso ya turata wurin wata mata daya gani a shagon amma inaaa taki. Da kyar ta gaya mishi sunanta, Faty.

Saiji sukayi baza a fitaba duk inda kake nan zaka makale. Wani abin mamaki tunda gadafi ya shigo shagon, duk wayanda ya kira bata zuwa, yaga missed call daga babanshi amma inya gwada sai taki zuwa, kuma yana kallon kowa nata waya da 'yan uwa da abokan arziki amma shi nashi bai zuwa. Har aron na mutane yayi amma inaaaa kaman wanda akama baki. Haka kullum yaketa trying ko zai samu.

Abinci da kyar yake samu donko kowa fita yakeyi zuwa nema. Gashi dole ya nema na mutane biyu tunda yana tareda yarinya. Kwatsam saiji sukayi an bada symptoms na CD, jan idanu da busasshen baki. Tuni idanu suka juyo kan gadafi.

"Nifa haka aka haifeni da jan idanu, kuma ina shan sigari shiyasa." Kowa ya kama aikin gabansa. Gadafi ya tsani wurin nan da yake zama, ga wari saboda rashin wankan jama'a, shi kanshi tsami yakeji yanayi.

Yana cikin jin takaicin halinda rayuwarshi ta shiga sai kawai wayar abbas ta shiga. Wayyo Allah murna ba ako magana. Saida mutanen wurin suka sha annobanne ta tafi. Ashe Mutumin nan ya iya godewa Allah haka?

"Alhamdulillah alhamdulillah hamdin kaseeran mubarakan, don Allah saurareni abbas, wai, na gode Allah..."

Zayyad ya kalla gadafi cikin mamaki. Dama yaga halinda gadafi ya shiga na rashin samun kowa a wayanshi, harda wayan wasuma in yayi amfani da baya samu. Ya lura gadafi irin 'yan hutun nan ne. Gashi anan ya zama kaman almajiri, ya fita hanyacinshi.

"Nine, gadafine." Ya damki wayan kaman zata gudu. "Gadafi ruma, I really need your help don Allah." Ya saurara, Faty na rikeda kafarshi. "Ina rose city na makale wallahi, a wani shop tareda wasu, Allah ya so basu badamin cutar ba." Mutanen da sukaji abinda yace suka kalloshi. Dama bai musuba, sai iyayi da kaskanta mutane yake. "This bloody epidermic yayi getting dina stuck a wani unguwa..." Ya juya ga zayyad ya tambayeshi.

"Miye sunan unguwan nan?"

"Minor street", zayyad ya amsa.

"Wani minor street. Please abbas can you get me out of here?" Faty ta matsa tanata girgiza kafanshi. Ya tureta ta fadi, baima kulaba.

"On what!?" Faty ta fara kuka, wata mata tazo ta dauketa taki.

"Thank you so much abbas, please try harder, nasha wuya wallahi". Aje wayan keda wuya ya juya ya dauketa yayita bata hakuri har saida tayi shiru.

A exercise room, sanye da singlet baki da trouser da white snickers, hafiz na zaune rikeda karfen arm lifting yana dagashi sama da kasa, dad dinshi ya shigo. Hafiz yayi mamakin ganin dad dinshi a sashenshi. Duk sanda yake bukatan ganinsu, 'ya'yanshi, saidai su suje wajenshi bade shi yazo ba. Ya ajiye karfen a kasa ya maida hankalinshi wurin dad.

"Dad, what's up?"

"What happened between you and nadiya?"

"Nadiya?"

"Yeah, yarinyar danace you'll be meeting?" Dad yasan hafiz baya son auren dangi shiyasa ya fita daga dangi ko za ayi dace.

"Oh that one, dad mantata kawai".

Tayaya za ayi don taga dad dintane ke ruling dazzling city se tayita zuba ma mutane takama da iko iri iri, shi kuma dan ya zama banza saiya saurareta. Shi kanshi inda za a gwada iko yanada kusan 65% na dazzling city, amma yana takama da hakan? Sai wata rubbish dabama ita ke ruling garinba zatazo da takaman ita 'yar wane da wance, waye da waye, shiyasa ya fita iskanta kawai.

Dad dinshi yaso ya hadashi da 'yar ministan finance na dazzling city, amma sanin dan nashi yasa dole ya hakura. Dad ya kalla hafiz cikin damuwa. "All women are not the same hafiz, you have to learn to forgive and forget. Please hafiz I want a grandchild soon, kaji?"

"Yeah dad, sure". Yayi murmushi saida dimple dinshi ya lotsa. Ya dauka boxing gloves yasa ya tsaya wurin punching bag ya fara aika ma abin naushi kala kala, naushi daddaya ko bibbiyu ko uku uku. Fitan dad keda wuya abbas ya shigo.

Zufa dukya mamaye gashin kai da fuskan hafiz yanata kai naushi da karfaffun hannayenshi. Abbas ya samu wuri ya zauna yanata kallonshi harya dakata. Hafiz ya cire gloves din ya dauka towel dake ajiye a wurin ya goge zufan ya rataye towel a wuyanshi. Ya iso wurin abbas ya zauna ya dauka ruwa ya kwankwada.

"Assalaam, good morning handsome".

"Wa alaikas salaam, morning. Its your rest day, why are you here?"

"No inashane kawai kana bukatan wani abu....".

"Yaushe ka fara gulma?" Giran hafiz daya ya daga cikin tambaya.

"Nooo ba haka bane...". Ya dara.

Dama abinda ya kawoshi kenan yaji yanda aka kaya tsakanin hafiz da Asiya. Yasan hafiz bazai gaya mishi komai ba amma shi kanshi abbas yasan yanda zai samu labarin komai daga hafiz.

"Amma akwai saurayinda ya karya mata zuciya". Hafiz ya zare towel daga wuya yana saurare. "Shidai saurayin hala yazone da wata manufa dayaga ba haka Asiya takeba saiya janye bayan ansa ranan aurensu." Abbas yayi bayani.

"Wayeshi?" Muryar hafiz ta canza nan da nan. Waye wannan banzan dayazo yaci amanarta haka, no wonder the girl was so harsh daya fara zance da ita. Amma kila yamai daidai, donda yanzu wawan ya aureta daya jama hafiz babban rashi.

"Ruma, gadafi ruma".

"Mom, wallahi zan batawa farouk rai, ni abokiyar wasarshice".

"Uhm, kudai kuka sani, waiya inda kikene, ana kwashe gawan kuwa?"

Asiya ta leka ta glass balcony, yauma basu faraba da wuri, kila sai anjima don taga sunfi kwasa da yamma. Abin dai ba a cewa komai don dambun gawawwakine take ta hangowa.

"Eh da yamma suke kwasa, mom kince jiya an samu wanine ko wata mai CD, to ya aka karashe?"

"Hm gawanshi aka fidda daga gidan makotanmu, akayi sanitizing gidan. Ashe shi kadaine a gidan. Mutanen gidan inaga sunyi tafiya".

"To Allah ya kiyaye, ki tabbatarda farouk baya fita kinsan halinshi mom".

"Insha Allah, yanzu ya zama mace ai". Asiya ta kwashe da dariya. Wayarta yayi karan message. Tagama waya da mom sannan ta duba.

'One in d whole wide world, queen that rules ma hrt, good morning.'

Hm wannan mutumin again. Wai meyasa baya son gaya mata sunanshi? Golden gates corps? Inako ta taba jin wannan sunan? Kaman a dazzling city. Wait! Bari ta gani.

'Rouk, emergency kana kusa?' Bayan Minti biyu ya amsa.

'Sis, yadai?'

'Golden gates corps, inaka taba jin sunan?' Farouk yasan labarin duk wani maiji da fada a dazzling city kaman ma wurinshine taji yanata maganan son yin aiki a golden gate corps in ya gama school. Bayan mintuna farouk ya amsa.

'Dazzling city most famous science and technology company, known world wide cox they have branches all over the world. Main branch dazzle city'

Oh hakane, sunada branches ma anan rose.

'Sis, meyasa kike tambaya?'

'Nothing, just curious, wait! Handsome nekeda kamfanin ko?'

'Yeah'. To kode shine....noooo ita asuwa handsome yace itace tashi. Saidai in wanine mai mishi aiki bashiba gaskiya.

'Rouk, it is possible kaman ayi min message ta thisapp ba tareda wanda yayi yanada number naba?'

'Wake miki message?'

'Just answer me plz, I'll tell u'.

'Not that I know of, I don't think so. Saidai inya kware a computer gaskiya, so wayeshi? Badai shine golden gate corps dinba?'

'Shifa, yaki ya sanardani yanda ya samu number na kuma yaki gayamin sunanshi'

Nan Asiya ta kwashe zancen da sukayi ta gaya mishi of course ta boye wasu abubuwanda ya gaya mata, kaman maganganun cikin chats din. Farouk yace mata tunda golden gates sun kware a computer, so zai iya yuwa wani ma'aikacine na golden.

Yanzu za ayita da gwajewa, don yau tana bukatan amsoshi kuma dole ta samu inba hakaba ya tafi ya bata wuri.

'Morning, tell me who u are plz'.

'Before I do that, I need you to do something for me baby, plzzz'

'Idan bazaka gayaba sai an jima'.

'Wait plz, am handsome, Hafiz Mahmoud handsome'.

Wayan asiya ta kusa subucewa daga hannunta. Minti daya shiru, Minti biyu shiru. Hannunta na rawa ta fara typing.

'Nice joke, goodbye'.

Ta sauka daga grammagram, social media ne.

'Rouk, its him, but am not sure, what to do?'

'Him who?'

'Handsome mana, amma yazan san lallai shine?'

'Video call'

Hakane video call de ba karya. Tana zaune a couch a boss office, tana kara kimtsawa tana mikarda rigarta, karamin farin hijabinta, tana jiran video call daga handsome. To meyasa gabanta keta wani faduwa? Har wani amai amai takeji. Wayarta tayi kara saida zuciyarta ta tsinke, ta kalla screen ta saki ajiyar zuci ta dauka.

"Assalaam alaikum...".

Kyakkyawan fuska ta bayyana a screen, idanunshi farare tas bakin kuma wuluk, dogon hanci daya kusa kai baki, bakinshi wow! Mai fadi dadidai fuskarshi. Sajenshi siriri da gemunshi guntu, gashin kanshi baki wuluk mai kyalli, daga gani sai yayi laushi...

"Hello?" Hankali ya dawoma Asiya taji kunya, tayi sauri ta sadda idanu. Hafiz yayi murmushi. "Yanzu de kin ganniko, so this is no joke, baby."

Ai tana ce mishi bye, ya rude ya isheta da message iri iri har saida ta bashi amsa. Tace mishi sede suyi video call to make sure shine da gaske, da gudu ya yarda.

"Wa alaikumussalaam. Um....handsome?"

"Yeah babe, how are u?"

"I'm good."

Wani mugun farin cikin ya baibaye zuciyarshi, ashe wata mace na iya sashi jin haka kuma? To lallai ko bazai barta taba, aishi ya riga ya samu ko tanada saurayi bai damuba saidai saurayin ya hakura. What a beautiful lady, muryata kaman yayita saurare har abada, to ya akayi tayi shiru? Oh ashe shine zai cigabada da magana.

"Its a pleasure meeting you, kina pharmacy har yanzu kenan?"

"Yeah"

"Wane pharmacy, what's the name?"

"Ahmed pharmacy."

"So Asiya liman, you are talking with hafiz, from dazzling city. Saw your video, and am a goner." Tayi murmushi ya kallo dimple dinta kaman irin nashi.

"I know the Internet has so many version of my story, but I want to tell you who I am personally."

Hafiz ya taso shi kadaine namiji a gidansu, ya fara mata bayani. Mahaifinsu matarshi daya itace mamansu, su biyarne wurin iyayensu. Shine babba sai imaan, khairat, zakiyya da raihana. Dukkansu kasan waje sukayi karatu both boko da islama. Ya sauke Qur'an yanada 16 years. Ya fara hadda ya bari yacigaba da karatun littafan addini kawai. Information technology ya karanta kuma yayi masters akai.

Yanada son yaga mutum mai kwazo a rayuwarshi, baya daidaita da raggo, in bakada gaskiya, cuta ta maka yawa toka san inda dare yayi maka. Hakan yasa mutane ke tsoronshi da taka tsantsan dashi a ko'ina, gida da waje.

Baya son makaryaci, maci amana, inya kuskura ya kamaka da wadannan abubuwan ka kade. Ba babba ba yaro duk saita mutane yakeyi. Shiyasa yayi masoya da makiya da yawa. As long as yana kan gaskiyanshi to kowama bai isaba.

Yanada laushin zuciya ga wadda ta mamaye mishi ita, da tausayawa da hakuri. Tun lokacinda ya ganta a video da tayi yaji kawai dolene yasan wannan yarinya mai hankali da tausayi. A kalla, kullum saiya kalla video sau uku ko hudu. Shakuwa da kewanta sukayi mishi kanta a zuciya har yaji tako yayane saiya hadu da ita.

A kamfaninshi akwai communication center, tananne ya samu lambarta ya turo matada messages. Yaushe zai gaya mata illegal ways din dayabi wurin samun lambar. Wasu gaskiyan dolene a boyesu.

"Can I ask you something?"

"If you are going to ask ko inada saurayi, answer is no kuma gaskiya not anytime soon".

"Why? What happened baby, talk to me."

"Just."

"Dole akwai abinda ya faru for a beautiful girl like you ta kulle zuciyanta ma kauna."

"Abinda kawai zaka sani kenan."

"Don Allah ki gaya min, ko zanta damunki saikin gaji kin fadi."

"Aiko ka samu aiki."

"Don't you know, aiki inde akankine I don't mind doing it ko tsawon shekara nawa ne, I won't hesitate to do it." Wow! Nice English. Kaman daga can.

"Hmm am tired, need to go."

"Alright baby, sai yaushe kenan?"

"Well as you can see, ba wani aiki nakeyiba nan. Feel free to call anytime, amma next time inaso inji manufarka gareni."

"Insha Allah sweety, I will tell you everything, have a nice day."

"You too."

"Thanks, baby."

Asiya ta kashe kiran ta kishingida da kujera, rungume da wayan a kirji.