webnovel

TA ISO

A deadly virus was detected in rose city and kills people within seconds. The government issued a state of emergency until a cure is found. A handsome zillionaire volunteered to find the cure, in the process he met Asiya the gorgeous pharmacist who was stuck in her work place due to the government orders. Love builds between them as the virus kills and threatened to wipe out the entire city. However, the cure brought them closer and then........

Fatimazahra35 · Urban
Not enough ratings
20 Chs

BABI NA SHA DAYA SHAKUWA A ANNOBA

Abbas ya kalla hafiz cikin mamaki, bai taba jin hafiz yayi irin wadannan kalamai ga wata 'ya mace ba, even waddata karya mai zuciya bata samu wandannan kalaman masu nutsarda zuciyaba.

* * * *

Hafiz ya Addabi abbas ya siyo mishi ice cream, tun jiya yaketa azazzalanshi. Abinda yasa bai siyaba yasan wadda za a kaima. Shi tun asali bata yimaiba, kyakkyawace fara tas amma zuciyarta kwadayine zalla bason hafiz takeba amma mutumin ya kasa ganewa. Koya gane yaki ya yardanema ohon mishi.

Sun haduda fadilane a grassland city, sanda yaje attending wani meeting. Itace 'yar managing director din glass company da suke meeting da. Lokacin IT student ce amma tana shiga meetings saboda itace zatayi gadon kamfanin baban don itace kadai ya haifa.

Shigansu conference room din keda wuya idanun maiyar sai akan hafiz, kallo take angulun ko kifatawa batayi. Tsantsan kwadayine dirke a idanunta sanda take kare mishi kallo tsaf daga sama har kasa. Ga gogan in yayi dressing har maza saiya kunyata.

Bayan meeting din, da gangan ta rike wani file daya kamata ta bashi in an gama, ta biyosu cikin sauri da wani muryarta kaman gyare tana ihun a tsaidasu. Ta tako cikin rangwada da kararraya kaman wata wadda kugunta ya karye tana bashi hakuri ta mika ma hafiz, abbas zai karba file din don duk particulars din hafiz na hannunshi amma yakucacciyar ta janye hannunta ta turama hafiz file a kirji, tana wani marmar da ido tana murmushi kaman kura.

Ai tun a san abbas yasan hafiz ya shiga tarko. Ya samo glue, super glue ma. Tun a san ta addabi rayuwar abbas, saboda duk wani abinda saurayi zai siya donya birge mace shi ake sawa yayi. Advice, dole ya bada wacce tayi dadidai da yanda akeson jinta.

Fadila ta hure ma hafiz kunne bayajin shawaran kowa sai nata. Da rawan jiki hafiz keyin duk abinda tace. Maganganun abbas na gargadi tashi suke a banza Inba fifitata da yabata yayiba. Abinda hafiz ya kashe akan yarinyarnan ko abbas dakeyin aikin bazai iya fadiba.

Bacin ran data sa mutane daga iyayenshi har mutanen arziki ba ako magana. Inba hafiz ba bata ganin mutuncin kowa, kuma abin takaici shi hafiz din kaman ta rufe mishi ido baya ganin laifinta ko kadan. Babuma wanda ta raina kaman abbas, har direbanta ya zama don nuna isa da ikonta.

Yasha wulakancinta harya gaji. Kai! Har kusan rabashima tayi da hafiz don tace ya kaita salon kuma hafiz ce mishi yayi gidan kawarta kawai zai kaita. Kaman wani dan aikenta, tana bashi odan yakaita salon. Yace shiba inda zai kaita yade kawota gidan kawan ta fice ta bashi wuri.

Nan take ta kira hafiz tana kukan munafunci, zuciyan abbas tayi sama dayaga kiran hafiz nan da nan. Cin mutuncin da hafiz yayi mai har yau bai mantaba. Meye amfanin zaman abbas da shi Idan bazai iya farantama budurwarshi raiba? Meye baya mishi da dan wannan abu kankani zai gagareshi yi? Meyasa yake tozartashi yana nuna halin kankanta a gaban budurwarshi? To ya sani inhar ya fiddata daga motarnan, ya neman wani boss badai shi hafiz ba.

Tabdi! Zuciyar abbas kaman ta fashe saboda takaici da bacin rai. Har makoshinshi ya wani bushe, idanunshi suka kada sukayi ja. Amma me 'yar banzan tace daga ganin ya ajiye waya, waita sauka dinne? Abbas ya fizgi mota cikin fushi suka bar wurin.

A hakan hafiz yazo mishi da mummunar labari, waishi zai tura gidansu fadila neman aurenta. A ranan saida kan abbas ya kusa harbawa. Waima ya rasa wadda zai aura sai mara mutuncin nan. Aiko bade in abbas na rayeba wallahi.

Da azabanta ya ishi jama'a, ai saida suka san yanda sukayi da ita. Ai amfanin technology kenan. Video yayi nata tanama manya rashin kunya tana cin mutuncinsu. Tana wani bugun kirji ita ta kusa zama Mrs handsome. Bata san tarko aka hada mataba. Abbas aiyasan abinda hafiz ya tsana, sorry her.

A cikin hadin tarkon harda tsoho yayi kuka amma ko a jikinta illama ta hahhado mishi da zagi. Perfect video kenan, haka yayi compiling ya rufe ido ya turama hafiz ta wata sabuwar waya da number. Don zakin zai gane shine ya turo in har yayi amfani da wayanshi. Kwararrene a computer field.

Abinda yayita hadawa kenan shiyasa bai siya ice cream dinba amma yanzu daya san ya hado bom saiya siyo vanilla and cherry ice cream babban roba yazo dashi sashen hafiz a gida. Shiganshi keda wuya ya hango hafiz na kallon wayanshi, giranshi a hade, idanunshi sun canza launi, hannunshi damke da wayan kaman zai fasata. Abbas yayi murmushi kadan a boye ya karaso ya zauna yana fuskantar hafiz.

"Handsome ga sakon, yaushe zamu kai mata? Tunda tare zamu yau kace."

"Watch this." Ya cilla mai wayan, abbas ya cafke hadda nuna mamakin halinda hafiz ya shiga kaman bai san abinda zai faruba kenan. Yaga fadila ta fito tsakar gidansu tana kararraya tana waya da wani tana kiransa love tana ce mishi karya damu zata cizga na cizga daga wannan wawan handsome din, ko bayan auren nema zasu cigaba da haduwa ai. Tayi dariyan takama tareda kissing waya harda hadowa da I love you.

Ya kalla ya kara kallo sannan ya kalla hafiz, idanunshi hafiz din sunyi ja. "May be an samu mistake....." Wayyo kaman kar yace hakan hafiz yayita bambamin bala'i, yana jin haushi yana ganin laifin kowa da ba a sanar dashi hakaba tun farko. Daya sauko daga fushinne abbas yayi mishi bayani dalla dalla ya gane ya roki gafara. "Ice cream dinfa?" Harara ta bashi amsa, ya murmusa.

Kaca kaca hafiz yayi da fadila dama ya iya rashin mutuncinshi inya tashi sai kace mema yasa ka sanshi. Yaune rana ta farin ciki a wurin abbas don shi ma saida ya sauke wani fushin akan ta, a cikin gidan iyayenta. Asirinta ya tonu tayita borin kunya.

Ita wallahi mutum yayi kadan su shigo har gidan su suna mata sharri suna ci mata mutunci, abbas ya nuna mata video ai seta kara fusata. Don rainin wayo wato har gidan su aka shigo aka musu labe! Mutanen banza, marasa tarbiyya...

Hafiz ya katseta daya tako gabanta cikin dakika daya, kawai ganin mutum tayi dab da ita tayi tsit. Wace mai tarbiyyace zata dinga neman hulda da wani namiji bayan aurenta? Ya fara reto mata bayani. Wace macen arzikice zata dinga zagi dacin mutuncin dattijai dana gaba da ita? Wace mace mai hankalice zata dinga daga murya tana karya ko kunya babu tace an mata sharri bayan ga evidence karara?

Yayi murnan ganin hakan ta faru a wannan lokacin ba saiya auretaba ta zama akuyar hanya kowa tabawa yakeyi. Ran farida in yayi miliyan ya baci, ta kallo hafiz cikin bacin rai ta kuma kasa cewa komai don yafita jin takaici da haushi lamarin.

Bugu da kari gashi kusada ita tana tsoron kadaya ya kai mata mari, dukda bai taba daga mata muryaba balle yasa mata hannu a jiki. Yace mata aure tsakaninsu babu, kuma baya bukatar ta maidoda kudinda ya bata na lefe. Halinta shi zai ruguza rayuwarta gabaki daya. Yafi karfin lalatatta bodara irinta, baya bukatan mace mara tsoron Allah mai cillarda gaskiya.

* * * *

Murmushi abbas yakeyi baima saniba domin tuna ranan rabuwar hafiz da fadila abin farin cikine gareshi.

"Me kakema murmushi bas?" Hankali ya dawo mishi. "Nothing, soyayya, I just want you to trade carefully, kasan abinda ya faru wancan karon."

"Thanks for reminding me, but this time I feel it's different."

"I hope so". Can ya tuna wani abu. "Handsome, ruma fa?"

"Ka barshi can ya rube a rose city ne ko town." Abbas ya kwashe da dariya mara kara. "Ka canza kenan?"

Kamshin fried rice da veggies ke tashi a kicin din Ahmed pharmacy. Asiya na soya kwai ta ciro plate ta zuba abinci ta daura kwan a sama ta kashe gas. Ta zauna a tebur a kicin ta fara ci.

Gaskiya ba karamin mamaki tayiba da sukayi video call da hafiz, domin bata taba tunaninma haka zai faruba, ai tana sha sai larabawa suke aure, kodayake shida kanshi ya sanar mata da cewa a web akwai labarinshi kala kala amma shi zaifiso ya gayamata labarinshi da kanshi.

Yanda yake tafiyarda rayuwarshi yana burgeta, ba a taba samun shi da karyaba, ko rashin gaskiya yana alfahari da hakan kuma daidai kenan. A wannan zamani sai kaga mutum yana sabon Allah yana alfahari da hakan saboda jahilci ya cika kan fam. Kuma irinsuma sai kaga ana aurensu, while mutanen arzikin sunata wahalan neman aure. Meya kawo haka? Ko yawaitan jahilanne da karancin masu ilimi?

Koma dai meye, samun saurayi kaman hafiz sai an bincika an tache an tsince an rege, ga ilimin islama ga boko ga sanin yanda zai tafiyarda rayuwarshi a duk inda ya samu kanshi. Jidai, da wanine yanda take mishi da tuni ya nuna girman kai ya rabu da ita tunda de ba itace autar mata ba. Ko a kalamanshi zaka san akwai hikima a ciki. Bata dai gama saninshiba amma tanaji a jikinta ya banbanta da sauran maza.

Ya hado abinda duk wata mace ke bukata. Ga kyau kaman wata, haske kaman rana, kudi kaman ruwa, ilimi kaman....kai yadai hadu kawai ta ko'ina. Wai ita yau Asiya liman tayi capturing zuciyar irin wannan saurayin!

A rayuwarta tana kaunar ta samu miji mai tsoron Allah da kiyaye dokokinshi mai kaunarta, mai girmama magabata, mai son al'ummansa musulmai, mai kyautatawa tsakaninsu, mai kwazon neman na kanshi, mai hakuri da tausayi, mai tawakkali. Ai samun irin haka sai an tona gaskiya, to amma meyasa takejin hafiz na daga cikin sahun wannan mutum da take nema?

Kwaso iska kawai tayi a spoon ta kai baki, dubawa keda wuya taga ashe ta cinye abincin. Lallai hafiz ya tafida tunaninta. Amma wani hanzari ba guduba, infa ya zone kaman gadafi? Ya nuna kyawawan halaye ashe na ciki na ciki. Anya, da gadafi yazo tana a high alert harse ranar da suka rabu, amma with hafiz hankalinta kwance yake amma bazatayi saurin yanke hukunciba.

Ta tsani samari wadanda hannunsu baya tsayawa a jikinsu, abinda ya fara hadata da gadafi kenan. Ta tsani me shan taba, gadafi yayi karya ashe yanasha. Dukda haka tanata tura kanta taga de tayi auren nan da kowa ya kosa tayi, Allah ya taimaketa shida kanshi yace ya fasa.

A ganinta tun daren dayazo wurinta yayi yunkurin taba mata jiki ta haushi da bala'in masifa da wa'azi don kar yaga ya kusa aurenta yayi tunanin zai iya komai, tuni ta taka masa birki. Har shock yayi dayaga reaction dinta, daga baya yayita bata hakuri. Tofa tun wannan dare ya fara rashin daukan wayarta, rashin kiranta, rashin yi mata wasika. Daga baya yace ya fasa.

Ta shiga halin takaici da bakin ciki, da bacin rai amma mai tayi? Saita kaima Allah kukanta, tayita rokonshi ya sassaita mata zuciya sannan ya kawo mata miji nagari. Tayi hakuri ta zubama sarautar Allah ido. 'Yan uwa sunyita maganganunsu sun gaji gameda ita har yanzu bata samu mijiba. Shekaru na tafiya, yanzu 25 take. Wasuma har cewa sukayi ai tana jira mai jirgi da motane amma ko a jikinta. Biyema mutane irin wadannan ba abinda zai kai mutum sai ga bacin raima.

Dad yabata kwarin gwiwa wajen kwantar mata da hankali, wani baya auren matar wani. Lokacinta na nan zuwa, kuma in yazo, zai nunama mutane iya gajen hakurinsu. Mom da farouk are the best wurin sata ta manta da wancan wawan. Hardai farouk shiya nuna mata wawan does not deserve her, baima dace da rayuwartaba and he's right. Yanzu kam sakau takeji.

Kyakkyawan fuskan hafiz ta mamaye ma Asiya tunani, tayi ajiyan zuci har saida taba kanta dariya. Wa zata gayama halin farin cikin data shiga? Batada kawaye sai 'yan uwa, saidai ummiri kuma dagantakarsu irinta boss ne dana kasa dashi. Farouk kuma gaskiya bata shirya gaya mishiba dukda yasan hafiz na zance da ita. He is very protective of her tun sanda ta rabuda da wawan can. Kota kirashine? Kai a'a. Kodai ta mai text, kai anya?

'Ummiri u dey?'

Eh mana ya kamata tadan kauda kai daga tunaninshi. Kaman zata iya, saidai ta kwatanta, shiyasa take chat da ummi.

'Asiya ya kike?'

'Lafiya lau'.

'Ya kike ji da kadaici?'

'Gameda wannan, ina bukatan shawarane. Menene kikeyi a lokutanda kike ke kadai?'

'😀 da gaske?'

'Nidai ki gayamin'.

'Read Qur'an, play games a wayanki, chat with ppl, sleep, roam around the pharmacy, watch t.v amma ba news ba. Ko duk kinyisu?'

'Inaso in dinga ganin update akan CD shiyasa nake kallon news'.

'Of course zaki kalla amma ba koda yaushe ba ai'.

'Me kikeyi yanzu?'

'Game ma nakeyi naga text dinki'.

'Um... Ummiri kinada saurayi?'

Zaman kadaici nan babu dadi, wani abinda baida dadi wasu lokutan shine rashin kawa, Asiya batada kawa ko daya tun sanda tabar school. Dayake duk kawayenta na university of rose, daga wasu jihohin suke. Asalima batada kawanda zata shawarceta akan abubuwa muhimmai kaman de wannan zancen hafiz din da dole yasa take tambayan ummi gameda lamarin.

Bazata iya tuntubar mom ba akan maganan da bai mayi karfiba tukun. Farouk kuma akwai zafi, don tun sanda gadafi ya rabu da ita, farouk C.I.D yake zama inya ganta da saurayi, koda ba saurayinta bane sai tasha tuhuma. Kuma wasu maganganun sai mace da mace, ita zatafi gane halinda ake ciki tabata shawara akai.

'Hmm meyasa kika tambaya?'

In hafiz yasaka gaba ai dole ka fara tambaye tambaye. Tayima ummi bayanin wanine yaga video dinta shikenan seda yasan yanda ya samu lambarta har sun fara chat. Amma abin shine, Asiya taji ya kwanta mata...

'Wait, daga chatting kawai kin fada?'

Ummi tayi mamakin jin Asiya na neman shawaranta akan saurayi. Bata taba ganin koda a kuskure wani yazo wurin Asiya ba a wurin aiki, bata saniba dai ko a gida amma a idonta, ko wayan soyayya bata taba ganin Asiya nayiba. Always business kawai haka take ganin Asiya. To yau kuma gashi tana neman shawara akan saurayi? Ummi zataso ganin wannan daceccen mutumin.

Asiya tayi mata bayanin video call dinda sukayi, ya dai nuna sha'awarta amma baiyi magana sosai akan manufarshi akantaba. Yanda ya kwanta mata rai daga kalamanshi kawai ji take kaman ta kira wayarshi kota mishi message, kawai de taji wani abu dagashi.

'To meye na zumudi haka? Kifa ja ajinki ke macece, kada ki dinga shisshige masa da yawa, maintain boundaries please.'

Toya zatayi da zuciyarta dake kewanshi? Wallahi a yanzu haka kiris ya rage ta danna masa message...

'Kadaki kuskura na gaya miki, sufa maza ba a shige musu farat daya. Tunda baku dadeda haduwaba, kiji abinda yake bukata dake tukun, sanna ki hadudashi physically don even the video can be deceiving.

Deceiving ta ina? inda ummi tasan maf'ulun bihi din da batace hakaba ai. Haduwa dashi zaiyi wuya, tayaya za ayi ta iya jira harsai sun hadu bayan tun yanzu tana jinshi a ranta yanata mamayewa? Ummi ta cigabada lecture.

'Kawai ki nuna mishi kaman baki damu ba da maganan dazai miki, 100% fa zaki maida hankalinki wurin sauraren duk abinda zaice, ki rikesu in details kuma don zasuyi amfani nan gaba. Ke kuma ki fayyace mishi tun farko abinda kike so da wanda bakiso, ki gaya mishi akidar gidanku da yanda al'adun gidanku suke. Sannan ki nuna mishi daraja da mutuncin gidanku a idonki. Nufina iyaye da 'yan uwa.'

Wow! Yarinyar ta iya bada shawara, kuma kawai 2 years asiya tabata amma tanada kaifin tunani. Of course baza taso tayi saurayinda bazai girmama iyayenta ta 'yan uwantaba, amma gameda al'adun gidansu wannan ba matsala bane. Gwara da tayi mata magana, zata tuna ta sakoshi a zance in lokacin yayi. Abubuwa da yawa akwai su kam a list dinta na ki. List na so kuma saita binciko.

'Ki bada gaskiya a cikin relationship dinku kuma ki nema gaskiya daga gareshi. Karki kuskura ki koya mishi karya don inna Allah yayi ya zamo mijinki bakiso ki samu matsalan karya taredashi. Allah taimaka.'

'Nagode ummiri, u have helped a lot.'

'Keni dan tsananin kina kirana ummiri har a mafarki nayi kinata kwala min kira ummiriririririi.'

Asiya ta kwashe da dariya ta tura emoji din dariya. Ummi kenan, Aiko tayi kawa daga yanzu gaskiya.