webnovel

TA ISO

A deadly virus was detected in rose city and kills people within seconds. The government issued a state of emergency until a cure is found. A handsome zillionaire volunteered to find the cure, in the process he met Asiya the gorgeous pharmacist who was stuck in her work place due to the government orders. Love builds between them as the virus kills and threatened to wipe out the entire city. However, the cure brought them closer and then........

Fatimazahra35 · perkotaan
Peringkat tidak cukup
20 Chs

BABI NA BIYU ANNOBA TA BI GARI

Mijin yusrah na cikin mota, direba na tukashi, saiya taka birki. A gaba, mutane ne suka taru sun tare titi.

"Meke faruwa?" Mijin yusrah ya tambaya.

"Mutanene da yawa kaman wani abu ya faru. Kila accident ne".

"To amma sai su cika titi haka, bita gefensu harmu samu clear way".

Direba yayi horn yana bin gefen mutane a hankali har ya iso gaban wani police. Police daya lura motace ya iso wurin. Direba da mijin yusrah sukaja glass na window kasa.

"Officer, lafiya kuwa?", Mijin yusrah ya tambaya.

HONEY STREET

Mai rahoto na aikinshi, hankalinshi a tashe.

"Kuna ganin abinda ke faruwa kuwa? Mutanene kaman kwari se mutuwa sukeyi...ba a san musabbabin faruwan hakanba...". yaci tuntube da wata gawan be fadiba se ganin yayi me rikeda camera ya sulale kasa shima. "Innalillahi, Adam! Adam lafiya?!! ADAM!!!"

MARKET ROAD

Almajiri yana cikin bara ya fadi kasa. Sauran almajiran dake taredashi sukayita girgizashi bai tashiba. Kaman ana ruwan kwari, daya bayan daya sauran almajiran suka dinga faduwa matattu. Mutane suka fara rudewa, kowa hankalinshi a tashe. Wani mutum ya yanke jiki ya bige wata mata ya fadi, matar ta tsala ihu itama ta fadi matatta. Nan da nan unguwa ya hargitse, kowa na gudun kowa. Duk inda kake gudu ka haduda wani saika canza hanya.

"Wayyo Allah mun shiga uku annoba ta shigo gari". Fadin haka keda wuya mutumin ya rike wuya, kaman ana shakeshi ya fadi kasa a mace. Kowa ya kara kidimewa, guje guje ake tayi a gari.

"Oga please ku koma hanya da kun fito. Anyi blocking road dinnan". Police yace ma mijin yusrah. "Meke faruwane, meyasa akayi blocking.....? Ihu sukaji an kwala. Daya bayan daya mutane nata zubewa kasa matattu.

Police ya ruga yaga make faruwa, isarshi keda wuya shima yabi layin matattu. "Ishak, fita ka dubo abinda faruwa". Idanun ishak a zare. "Anya oga, kalla fa". Ya nuna gaba dashi ta glass din mota. A gaban idon mijin yusrah yaga police ya zube kasa, mutane sukaci gabada zubewa kasa. A rikice yacema direba subar wurin tareda jan glass na window sama.

Asiya ta fito daga office dinta, ta dauka wani magani tana dubawa. Ummi ta dawo reception kawai seji sukaji KIIIIYYYY GARAM!!! anyi hatsarin mota. Hankali tashe sukayi waje. Isarsu bakin gate keda wuya, samari biyu kan wayyo kudina suma suka fadi sede gawansune kawai.

"Muje mu taimaka musu.....". Ummi zata zura da gudu kenan Asiya ta damko hannunta. Yatsanta na rawa ta nuna gaba dasu. Mutane a mota zaune a mace, gefen titi, mutane sunfi a kirga kwance. Ko'ina yayi tsit. Asiya ta fara jada baya tareda jawo ummi suka ruga cikin pharmacy. Asiya ta rike kai da hannayenta biyu a rikice. Ummi tana kalle kalle a kidime ta kallo t.v, tayi sauri ta dauka remote ta kara murya.

".....the government is pleading with people to stay where ever they are till they found out the cause of this chaos".

Hankalinsu ya koma kan kallon gawawwakin mutane da ake nunawa kaman kwari, Kara zube. Kowane channel Ummi ta bude, abin ba dadin ji balle gani. "Inna lillahi wa Inna ilaihir raji'in, don Allah a kawo muna dauki, mutane sai mutuwa sukeyi haka kawai." Mai rahoto yace. Asiya da Ummi suka Kalla juna. Ya cigaba da bada rahoto hankalinshi a tashe. "Ni....ni kaina duk inda nabi gawa naketa gani. T...to....".

Wata mata ta rugo a guje wurin Mai rahoto ta na yarinyarta, a agaza mata yarinyarta sai kawai ta rike wuya ta fadi a mace. Mai rikeda camera ya sulale ya fadi a mace. Mai rahoto ya rude. "Sani! SANIIIII!!". Ya dauka cameran yana daukan kanshi. "Don Allah jama'a a lura, ku zauna a gidajenku... Ni...nina tafi. Daga nan baddo road". Yana Kuka yana magana.

"Innalillahi wa Inna ilaihir raji'in. Baddo road kusada layin mune amazon asiya. Zan tafi gida!!". Ummi ta suri jakanta ta zura a guje tabi hanya ta bayan pharmacy akwai exit. Asiya tabita a guje amma ummi ta riga ta isa karamin gate. Asiya ta hau balcony din bayan pharmacy ta stairs ta hango Ummi.

"Ummiiii kisa face mask!!!". Ta kwala ma Ummi kira. Ummi ta tura hannu jaka ta ciro face mask tasa tana gudu gudu. Mutane nata guje guje, tun Asiya na hango Ummi harta gushe. Ummi tabar karamin kofan a bude, Asiya tayi sauri ta sauko taje ta rufeda kwadon dake wurin, ta dawo ta shiga pharmacy. Ta ruga main gate tasa padlock, sannan tasa wani kwadon a karamin kofan shiga dake gefe.

Gaban pharmacy din glass window ne babba. Kofanma glass ne na shiga wurin saida magungunan, Asiya ta ruga ta janyo burglary daga sama ta rufe har kasa tasa padlock. Ta zagaya ta shiga ta baya ta kulle kofan bayan tasa sakata ta ciki.

Kirjinta bugawa yakeyi kaman zuciyarta zata fashe. Hannayenta se zufa sukeyi tanata gogewa jikin uniform dinta.

"We still don't know the cause of this epidermic, which is why we urge the citizens of rose city to please stay indoors to reduce this mass death". Asiya ta Kalla t.v. "Families should notify their loved ones outside the city not to visit them....". Aljihu Asiya ta tura hannunta ta dauka i phone dinta ta kira gida. Se zirya takeyi, ta samu kujeran reception ta zauna.

"Asiy.....asiy kina Ina!?" Muryar mom a rikice. Zumbur Asiya ta mike tsaye. "Wurin aiki mom, Ina dad da farouk?"

"Babanku yana nan bari ince mishi na sameki. Alhamdulillah...". Kara Asiya keta ji. "Asiya kina nan? Ga daddyn naki".

"Asiya kina Ina!!?"

"At the pharmacy dad. Dad meke faruwane a gari, ko'ina mutane se mutuwa sukeyi!!!?" Murya Asiya na rawa kaman zatayi kuka.

"Sweety, kwantar da hankalinki...". Tunanin dan uwanta ya fado mata. "Dad! Ina Farouk?" Ina yake!!?"

Farouk yaci gudu harya gaji, boots dinshi sunyi kaca kaca da datti. Kayan jikinshi duk sun canza launi. Zufa ya gangaro daga goshinshi. Yasa hannayenshi kan gwiwanshi, se nishi yakeyi.

* * * *

9am

Farouk yayi gayu ya shirya don zai hadu da wasu abokanshi daya dade bai ganiba. Sanyeda shirt ash me dogon hannu, bakin jeans da classy boot's, hannunshi daukeda dark smart watch, yasa Bluetooth earpiece. Idanunshi makale da dark glasses. Ya dauka mukullin bike dinshi ya isa open garage yasa helmet, abun kai. Ya tada bike ya bata wuta, ya fice.

Abokan da zai iske tare sukayi secondary, sun rabu lokacinda ya samu university a golden city, awa dayane daga rose city, yana karatun engineering. Yanzu final year yake, ya dawo hutune kaman yanda ya saba.

Beet street

Samari uku na zaune a karkashin bishiya a dakalin kofar gidansu muhsin suna hira, sega saurayi ya doso da gudu kan bike, yana isowa inda suke ya rage gudun ya tsaya. Hankalinsu ya wuce wurin son ganin wayeshi. Ya cire helmet ya ajiye sama kan bike, ya kallesu tareda murmushin gefen baki.

"Bura ubannan dama kaine!!?" Saurayi na farko ya taso suka sha hannu. "Gaye ashe ka shigo gari". Saurayi na biyu yasha hannu da Farouk. "Kaman nasan zan ganku nan. So how's it going guys, muhsin, Faisal, zaks". Suka zazzauna.

"It's cool. So ya school?" Zakari, short for zaks ya tambaya farouk suna shan hannu. "Wow, very hard but am pulling through, ba damuwa".

"Kaifa yanzu ka zama ALAJI Farouk.....". Faisal yace ya na ta watse hannayenshi. Sukayi dariya, kwatsam se ganin mutum sukayi a firgice yana gudu gudu.

"Samari ku gudu annoba ta shigo gari, ku ceci kanku ku gudu.....". ya gudu yana sambatunshi harya bace daga ganinsu. "Wow! people now a days are whacked up in the he...". Farouk bai gama maganan da zaiyiba.

Mutane sun kusan talatin suka shigo layin a guje, a rikice, a kidime, wasuna kuka, wasuna a taimakesu, wasu jikinsu jina jina. Yara kanana nata ihu suna kuka. Daya daga cikin yaran ya fadi mace. "Annoban ta iso nan", Wani ya Kwala ihu. A gaban idanun farouk da abokanshi sukaga mutanen nata faduwa suna mutuwa, daya bayan daya seda suka tulu a wurin a mace.

Tashin hankalin dake rubuce a fuskokinsu ba a ko magana. Kaman an tsungulesu kowa ya kwasa kafa ya arta a guje. Tuni an manta da bike.

* * * *

Farouk ya mike tsaye yana kalle kalle baima san inda gudunshi ya kawoshiba, eye glass dinshi ya dade da barin idanunshi, bluetooth ear piece oho. Tunda ya fara gudu duk inda yabi gawa yake gani, ko yana kallo sai yaga mutane sun zube kasa a mace. Ya lura idan wani na kusa da mataccen shima saiya zube kasa, aiko ya kara wuta, shine bai tsayaba sai tsakiyar daji. At least anan ba mutane don bai hadu da kowaba tun sanda ya shigo.

Tafiya yakeyi a gajiye ga kishi, bakinshi a bushe. Can gaba dashi yaji karan ganyaye, kaman ana takasu cikin gudu, aiko ya canza hanya ya arta a guje.

Jikin Asiya ya hau rawa. Ta manna wayan a kunnenta. "Dad don Allah ka gaya min ina yake?"

"Asiy, yace zaije beet street ganin abokanshi, mun buga wayanshi bai daukaba har sedama mukazo bamu samunshi", Mom tayi mata bayani. "Fatanmu Allah dawo dashi lafiya", dad yace.

Hawaye suka gangaro kan kumatun asiya. A rayuwarta in akace mata zataga rana irinta yau bazata ta taba yardaba. Sun taso su biyu wurin iyayensu. Kauna, kulawa da dajin dadi duk suna samu daga wurin iyayensu. Asiya taba farouk shekara dayane kawai. Tana gama school ta samu aiki a Ahmed pharmacy, abokin babansune mai wurin. Dama burinta taga ta karanci pharmacy donta dinga taimakon al'ummah wajen kiyon lafiyansu kuma se burin nata ya cika.

Kaninta ya kasance yanada son gayu, son yin turanci, da tsokanta kaman me. Har Alla Alla take ya koma school in ya dawo hutu donko bazai barta ta hutaba. Ashe akwai ranarda zatayi kewanshi da ji mishi tsoron rasa ranshi. Wannan abu de ba babba balle yaro, kowa diba yake. Idanun Asiya sukayi kan t.v, inda ba labari sena gawawwaki.

"Kinaji Asiya?" Dad yace. Hawaye suka gangaro kan fuskan asiya tayi sauri ta goge. "Na'am dad?"

"Nace kadaki damu zamu san yanda zamuyi mu dawo dake gida mu nemo Farouk".

"Akwai abinci a wurin? Don bamu tabbatarda lokacinda za a fara fitaba". Cikin damuwa mom tace. "Mom akwai komai nan karku damu. Zan zauna, in sarari ya samu zan dawo. Amma kucigaba da neman farouk a waya kuna samun shi ku kirani don Allah".

"To asiy. Allah shige mana gaba".

"Amin mom. Zan kiraku anjima". Asiya ta katse waya ta gwada na kaninta still be zuwa. Tayi Shiru can ta dauka wayan tayi mai text. 'Ka kirani inkaga text dinnan ASAP'.