webnovel

TA ISO

A deadly virus was detected in rose city and kills people within seconds. The government issued a state of emergency until a cure is found. A handsome zillionaire volunteered to find the cure, in the process he met Asiya the gorgeous pharmacist who was stuck in her work place due to the government orders. Love builds between them as the virus kills and threatened to wipe out the entire city. However, the cure brought them closer and then........

Fatimazahra35 · Urban
Not enough ratings
20 Chs

BABI NA DAYA ANNOBA

7 am

"Good morning rose city, it's 7 am on Monday morning, welcome to the show and what a lovely day in the city, the temperature is 250c. With me today on the show is.....".

Budurwa ta wuce ta gaban t.v sanye da fararen kayan aiki, dogon wando, riga daidai tsayin cinya, kanta farin hula inda ya nuna tulin gashinta ta baya ta kama. Ta zauna a kujerar palo rikeda teacup, ta kurba.

"Asiy, yanzuma tea kawai zakisha, bazaki danci wani abinda ze rike mike cikiba?" Mamanta tana rikeda plate din chips da kwai.

"Mom, innaje can ma abinda zanci kenan. Da sassafe haka bana iya cin abinci sede abu ruwa ruwa haka, saboda ulcer na".

"To shikenan Allah baki lafiya". Ta wuce dining table ta ajiye plate din. "Amin mom". Asiya ta kurbe tea dinta, ta ajiye cup ta mike tsaye tareda daukan karamin farin hijab tasa, ta sagala backpack(jakan baya) a kafadanta daya. Asiya ta dauka keys din mota, ta fara dube dube cikin sauri tana duba time. Ta shiga daki ta duba socket ta dawo palo ta duba socket.

"Wai ina power bank dinane? Mtssww, bade farouk ya dauka ba kuma. MOOOOM kinga power bank dina!?"

"Baya cikin jakanki?" Maman ta Kira daga kitchen. Asiya ta saukarda jakan ta duba can kasan jakan ta zaroshi. Hijabinta na sallah ya bullo ta maida, tayi zipping jakan "Mom zan wuce aiki". Mom ta iso palo.

"Kinga power bank din?"

"Na gani". Ta murmusa tana sa farin cover shoes, loafers.

"Shine za a kalawa dan autana".

"Uhum wannan gandareren ne dan auta. Lazy boy ko tashi daga bacci beyiba". Asiya tayi hanyan waje.

"A bar min da yayi baccinshi, ya dawo daga school, tafiya mai nisa....".

"Nan da golden city ne nisa? Wallahi mom kina shagwabashi, saina dawo".

"To asiy a dawo lafiya Allah bada sa'a". Ta kulle kofan palo.

"Amin". Asiya ta danna remote din mota ta bude kofan tuki ta wurga jakanta seat din gefe ta shiga ta rufe ta tada mota ta fice.

* * * *

Tsaye bakin titi, budurwa sanye da uniform din asibiti, hijab karami, farin riga guntu, skirt mai tsawo har kusan kafarta, fararen takalma. Tana rikeda jaka baka tana jiran napep. Ta tsaida wani me mutum daya a ciki.

"Ahmed pharmacy".

"To shiga muje". Ta shiga suka wuce.

Kaman ko wace safiyan litinin, an tashi a garin rose da hayaniyan motocin gida dana haya ga napep da bikers, da mutane wasuna tafiya zuwa aiyukansu wasuna bude wurin sana'o'insu. Yara sunata haraman zuwa school, almajirai nata harkokinsu na bara.

Magidanci dattijo na zaune akan dining table yana Karin kumallo. Yana hango t.v dake palo.

"....the situation here at knight street is confusing...." Me labarai tana fadi a t.v.

Magidancin nata kallon t.v yana cin abincinshi. Matarshi dattijuwa tazo ta zauna ta fara diban abinci.

"Nayi mafarkin yau ka makara".

"Hum". Yana kurba tea. "Wani abu ya faru a knight street....".

"Meya faru?" Ta gama sa abincin a plate. "Bande ji farkonba, amma naji suna cewa mutane uku sun fadi akan titi".

"Accident ne?"

"Haka kawai suna tafiya suka fadi, kuma ba tarema sukeba".

"Toh Allah sawake, gashi ko unguwansu najlah ne. 'Yar Cousin dita da tayi aure". Ya gama breakfast ya tashi. "Yusrah kin kunna heater kuwa?"

"Na kunna ai, rannan ma akasi aka samu". Ya girgiza kai yana murmushi ya wuce.

AHMED PHARMACY

Pharmacy ne babba me zaman kanshi a bold street. Gidan sama hawa dayane, kasa reception, da inda ake saida magunguna a gaba, akwai wata kofa a gefen kantan magunguna da zai kai office din Asiya. Store da toilet a lungu. Sama kuma, office din director ne da office din manager, sai conference room. Akwai kitchen me fadi tattareda kowane irin kayan kitchen daga utensils zuwa electronics. A waje akwai security room inda masu gadi ke ganin duk abin da ke faruwa a reception da kewaye da pharmacy din, dayake building din zagaye yake da cameras.

Motar Asiya na shiga gate din ahmed pharmacy inda take aiki as pharmacist, me bada magani. Maigadi na tsaye gefen motan cikin uniform dinshi ya tsayar da ita.

"Ranki ya dade, Ina kwana?"

"Lafiya lau, usama ya aiki?

"Alhamdulillah, don Allah alfarma nake nema".

"To usama ya akayi?"

"Matatace aka bugo tun asuba ba lafiya. To kuma ni kadai nayi shift jiya, ba halin inje. Salihu, wanda ze karbeni har yanzu baizoba. Na Kira wayanshi amma a kashe take". Giran Asiya ya hade cikin damuwa. "Tana gidane?"

"Dazu nayi waya sunce sun kaita asibiti, general".

"To jeka kawai tunda nazo, nasan shima salihu na hanya, kome ya tsaidashi oho".

"Godiya nake ranki ya dade".

"Allah bata lafiya".

"Amin". Asiya taja motarta wurin parking. Ta ciro jakarta ta shige cikin pharmacy din.

"Ina kwana ma?"

"Laaafiya lau, ummiri. Kin shigo kenan". Ummi nata kallo t.v tana gyara, tana kakkabe kuran dake kan magunguna a kantansu. Ummi ta murmusa. Pet name dinda asiya tayi mata kenan. "Eh wallahi. Yau kuma good morning din da abinda aka tashi kenan?" Asiya ta tsaya tana kallon t.v. Aka nuno unguwar soja mutane sun taru sun kewaye wani abu.

Asiya ta wuce ta shiga office dinta ta ajiye keys na mota da jaka. Office dinta me girmane ga fadi. Yana kunsheda tebur, kujeru guda biyu, parlor a gefe, shelf na books, kofan gefe kuma toilet. Asiya ta dauka remote ta kunna a.c. Files ta zaro daga jakanta, ta ciro hijab ta ajiye kan hannun kujera ta zagaya wurin seat ta zauna ta kunna laptop dake kan tebur.

Ummi ta rage volume din t.v a reception, taje tana checking new price list. A t.v aka nuna mutane sunfi goma kwance a kasa a honey street.