webnovel

TA ISO

A deadly virus was detected in rose city and kills people within seconds. The government issued a state of emergency until a cure is found. A handsome zillionaire volunteered to find the cure, in the process he met Asiya the gorgeous pharmacist who was stuck in her work place due to the government orders. Love builds between them as the virus kills and threatened to wipe out the entire city. However, the cure brought them closer and then........

Fatimazahra35 · perkotaan
Peringkat tidak cukup
20 Chs

BABI NA UKU DAMUWA

Wannan annoba daga ina ya samo asaline? Waye yazo dashi? Zuwa akayi dashi ko anan garinne yake? Nan garinne kadai ya sama ko da wasu garuruwan? Tambayoyin daketa yawo kenan a kan Asiya. Tanata zarya ta kasa zaune balle tsaye, can ta taka birki ta Kalla waje. Bude kofan bayan pharmacy keda wuya ta tuna wani abu, ta koma ta dawo sanye da face mask da hand gloves.

Katangan pharmacy din gajerene ana iya hango har tsallaken titi. Daga inda Asiya ta tsaya, hango gawawwaki takeyi. Ta hau stairs din balcony tana hango ko'ina daga sama, duka mutanen da taga sunata gudu dazu suna kwance a mace. Abinda ma yafi bata tsoro shine, gawawwakin ba adadi duk iya hangenta babu mai motsi.

Rufe hancinta ta karayi duk da face mask din dake fuskarta. Kafafunta na rawa ta sauko ta shige ciki ta garkame kofan ta jingina dashi, kirjinta sai bugawa yakeyi. Ji tayi kaman ita kadai keda rai a duk fadin unguwan. Kanta ya sara, cikinta yayi kugi. Shafa cikin tayi ta kalla saman stairs, ta cizge face mask daga fuskarta da sauri da hand gloves ta tura pocket, ta haura stairs se kitchen.

Zaune take kan karamin dining table a kitchen din, plate din chips da ketch up a gabanta ta kasaci. Kanta ya kasa sarrafa mata abinda idanuwanta da kunnuwanta ke gane da jiye mata.

Abinda zai iya kwasan mutane da yawa lokaci daya sede in a iska yake, wato airborne. Kuma it's the most deadliest disease don daka shakeshi an gama. A cikin kankanin lokaci zeyi awon gabada mutane dubu ma. Saide wanda Allah ya kubutarda.

Ina farouk yake? Wane hali yake ciki? Itafa? Ya zatayi ita kadai a wuri.....? Kuuuuuu, cikinta ya kara sakin wani kugi. Batasan inda Farouk yakeba ballema taje tazo dashi, ita kanta batama san yanda za ayi ta koma gidaba. Iyayenta su kansu hankalinsu ba kwance yakeba. Kwana nawa zatayi anan kafin dauki yazo? Inma zaizo kenan. Idan duka garin aka mu....ya isa hakanan. Duk amsoshin nan ba samunsu zatayiba, sannan tanata kara tsoratar da kanta.

Wayarta tayi kara, tayi sauri ta dauka daga kan tebur ta duba. Tayi tsaki ta ajiye, text message ne daga KTN, suna gargadin mutane da a zauna gida. Hakanan Asiya tayita tura abincin badan tana marmariba. Tsoronta daya duk sanda ta kalla wayanta, kadata kira ko a kira ace ba a ga farouk ba. Zumbur ta mike ta fice daga kitchen din rikeda wayanta.

Office din boss ta shiga dayake yana bata key. Office din na alfarmane, kato mai fadi, ga desk din mai kyau Mai tsada da kujerun alfarma. Palon daukeda couchs masu kyau da center table, kasanshi carpet ne mai laushi, gefe shelves, da slide glass balcony door. Balcony din zagaye da glass yake yanda idan ka fita zaka hango waje.

Idanun asiya sun fito ta sankare tana kallon gabanta. Dayake office din na kallon main gate. Mutane ne birjik a kwance nan ma ba adadi, tana iya hango yara, manya, mata da maza. Hawaye suka cigabada gangaro ba control.

Wayarta tayi kara. Da sauri ta ciro ta duba, tana share hawayen da bayan hannunta. Bata gane me lambarba ta dauka. "Assalamu alaikum".

"Wa alaikumussalaam, don Allah asiyace?" Asiya ta kara kallon lambar, ta kara a kunne.

"Eh, Waye ke magana?" Muryarta tayi laushi. "Matar Ahmed ce, yusrah".

"Um.....Ahmed?", ta tambaya cikin rashin fahimta.

"Boss dinku?"

"Oh aunty yusrah.....".

"Yana nan ne?" Zuciyar Asiya ta kara sama. "A'a, bai shigo ba.....".

"Na shiga uku, Inna lillahi wa Inna ilaihir raji'un".

"Wayanshi bai zuwane?" Bakin Asiya ya bushe da kyar ta hadiye miyau.

"Eh.....na shiga uku.....".

"Aunty yusrah kwantar da hankalinki don Allah nima zanyi trying dinshi".

"Oh yau munga tashin hankali. Kefa asiya, ya kike?"

"Kalau, muyita addu'an Allah dawo muna dasu lafiya".

"Insha Allah asiya, kema zan san yanda zanyi ki koma gida lafiya, Insha Allahu za a ga farouk. Kinji?"

"Nagode aunty yusrah, don Allah ki kirani in uncle Ahmed ya isa gida". Wayan na katsewa, Asiya ta nemo lambar Ahmed ta kira yana ringing amma ba a daukaba.

Motoci sun taru kan titi a chunkushe, mutanen ciki duk ba mai rai. Gefen titin gawawwakine, wasu rabin jikinsu na mota rabina waje, daga gani sunyi kokarin fitane lokacinda annoban ta auka musu. Mafi yawanci cikin mota suka mutu, kudaje sai bin gawawwakin suke suna ci.

Karan waya ke tashi a daya daga cikin motocin. Mutumin kanshi na jikin glass din window daya dan tsage. Jinine makale a goshinshi ya bushe. Idanunshi a rufe, wayan tanata kara. Idanuwanshi suka fara marmadi sai ya bude ido sunyi nauyi. Wayan tayi shiru, bayan 'yan dakikai ya mike zaune yana kalle kalle.

* * * *

Cikin kidimewa, ishak yaja mota da sauri yabar inda police din da sauran mutane ke mace. Yayita tsala gudu da mota, hankalinshi a tashe. Dukda a.c dake mota Ahmed zufa yakeyi. Ya dauka wayanshi, hannayenshi na rawa yana sambatu murya na rawa. "Naga wannan abu a t.v, ashe abin yayi worse haka!? In kira yus...." Ishak na shan wata kwana sai kiiiíiiii GARAMMM.

* * * *

Ahmed ya taba goshinshi ya dan yamutse fuska yaji wurin na zafi, ya Kalla hannunshi yaga bawon jini daya bushe. Idanunshi suka zagaya inda yake, ta glass window a waje , motocine a chunkushe, ya lura duka mutanen dake motocin basu motsi. Sune motocinda ishak yaci karoda. Ishak na gaban mota a langwabe, Ahmed na tsoron tabashi baisan ko sumewa yayiba ko abinda ya kashe sauran mutanene yayi awon gabadashi.

Wayar Ahmed ta hau kara, ya dudduba yana nemanta, ya zarota daga karkashin seat. "Yusrah....". Muryarshi tayi laushi.

"Alhamdulillah alhamdulillah Ahmed, ina kake? Meyasa baka dauka wayaba? Kako san meke faruwa? Ka dawo gida yanzun nan! Wai ina kakene?" Muryata tayi na kuka.

"Accident"

"KUKAYI!!!" Ina kuke? Zansa aje a daukoku". Ahmed ya kakkalla yana neman sign board. TRILLION STREET ne rubuce a jikin karfen.

Tunanin asiya ya kaita zuwaga Ummi tayi sauri ta kira lambar. "Ummi kece, kina ina?"

"Ina gida Asiya. Na iso lafiya kuma duk family house din kowa na nan".

"To alhamdulillah".

"Kefa? Bade kina can ba?"

"To ina zani? Nan yayi nisada gidanmu".

"Inna lillahi, to ya zakiyi? Kode kizo gidanmu ne.....".

"Ummiri, kwantar da hankalinki zan zauna nan tukun, in komai ya lafa dad zaizo ya daukeni".

"Kin tabbatar?"

"Karki damu....".

"Inde aka samu akasi don Allah kizo gidanmu". Asiya tayi ajiyan zuci. "To naji, take care". Lallai yarinyar taci arziki tunda ta koma gida lafiya lau. Yanzu farouk kawai Asiya ke jiran jin wani abu gamedashi. Kiran sallah ya fara tashi daga wayarta. Zuhur yayi, ta dauro alwala a toilet din boss ta fito taje office dinta ta dauko hijab ta dawo office din boss tayi sallah.