webnovel

TA ISO

A deadly virus was detected in rose city and kills people within seconds. The government issued a state of emergency until a cure is found. A handsome zillionaire volunteered to find the cure, in the process he met Asiya the gorgeous pharmacist who was stuck in her work place due to the government orders. Love builds between them as the virus kills and threatened to wipe out the entire city. However, the cure brought them closer and then........

Fatimazahra35 · perkotaan
Peringkat tidak cukup
20 Chs

BABI NA TARA NEMOTA

Wai ya akayi abin yakeda wahalane? Tun safe abu daya, inda ba hafiz ne ya bashi wannan aikinba kuma ya mishi gargadin da cewa shi kadai zai yishi wallahi da tuni yakaima Alpha team.

Alpha team karamin taron mutanene iyakarsu goma wanda suka kware a binciken asiri ta internet da fashin computer(hackers). Hafiz sukema aiki, a cikin dakikai kadan saisu samo maka duk abinda kake nema, komin security code dayake dashi kuwa. Su shiga, su dauka, su fita ba ama saniba.

Abbas ya saki tsaki cikin jin haushi. Mintuna nawa zasu dauka su gama. Amma shi awama nawa yayi. Suma suka sangartar dashi don shi ma he's very good a irin wannan aikin. Mtsw, hafiz ma saiya zageshi. Harya fara misaltawa irin ga hafiz yazo yana kallonshi. Yace mishi how many years yayi a course din daya turashi na computer dazai kasa yin dan karamin akin nan.

Yasaki ajiyar zuci ya ajiye note dinshi yana tunanin mafita. Ajiye note din keda wuya sai tayi kara. Yayi sauri ya sura ya duba, murmushi ya sauka akan lebenshi ya mike daga kujera a office din hafiz ya nufa computer room.

Computer room din golden gates corps office, wato wata duniyace ta daban na tsadaddun, advance computers da computer wares. Dakin nada girma sosai don zai dauka mutane kusan 500. Computers din dukansu screen touch ne, keyboards din soft touch ne mai kamada glass. Kowane aiki na creating(kekarowa), improving(ingantawa), producing(samarwa) ko developing(bunkasawa) software na normal computers kona wani software sabo na motoci ko jirage anan room din akeyi.

Shigan abbas yaga ma'aikatan dakin nata aikinsu, saiya hango hafiz tareda manajan kulada na'urorin computer room din. Suna gaban daya daga cikin computers din don manaja na nuna mai wani abu. Hafiz ya linke hannu daya a kirji, dayan hannu na karkashin guntun gemunshi, suna cikin tattaunawa mai zurfi.

Hafiz ya daga ido ya kalla abbas. Yayima manaja magana sannan ya nufo abbas. Suka fito daga dakin suna tafiya. Hafiz na gaba abbas na biye dashi.

"I've gotten what you asked fo.....".

"What took you so long?" Hafiz ya katseshi.

"Um.....problem". Hafiz ya kalloshi.

"Wane problem?"

"Technical", abbas ya amsa. Hafiz ya kara kalloshi ta gefen ido, ya juya ya mika hannu ya karba note din yana tafiya, abbas na biye dashi.

"Oh and for waisting my time, report to the task room". Ko kallonshi baiyiba ya wuce abinshi yana duba note. Abbas tuni ya taka birki ya sankare a wurin. Matsalan kenan, in bakayi abinda hafiz ya saka a cikin lokaciba, bazai bata lokaciba shima wurin punishing dinka. Task room ko punishment room.

Task room dakine da ake arranging kowane aikinda MD ya turo wato hafiz, don a turasu various units dinsu, of course ta computer. Tangamamen dakine, mai daukeda shelves sun kai 200 bangare daya, dayan bangare kuma kananan offices(cubicles) ne na ma'ikatan wurin, kowane cubicle daya yana representing din unit daya, units din sunkai 30, sama kuma office din manaja.

A cikin kowane shelf akwai task slides, kaman note ne amma na glass, it is transparent. Kowane aiki MD ya turoma manaja, sai manaja ya turama unit cubicle din task ta slides din, 'yan cubicle din saisu tura kowane aiyuka zuwa ga offices din daya dace aikin yaje.

Abbas ya fara danasani shigowa wurin. Saboda duk lokacinda yayima hafiz ba daidaiba nan yake turoshi don hafiz yasan ya tsana wurin. Gashi in ya kuskura ya sulale ya gudu, hafiz ya kamashi, tofa double punishment kenan. Next time inyace yazo da gudu zaije. Kai! Yama taba guduwa fa, labarin bamai dadi bane, ba a magana.

Manaja na tsaye a balcony a sama, gaban office dinshi ya hango abbas a kasa ya shigo task room, ya fara murmushi. Abbas yaji ranshi ya baci. Harda wani yima abbas marhaban dama yana neman karin hannu. Yanzu zaita azabtar dashi.

Hafiz na zaune a couch na office dinshi na alfarma yana kallon iPad, murmushi ya bayyana a lebbansa. Tun safe yake jiran wannan abin amma bas ya bata mishi lokaci. Pet name dinda yayima abbas kenan bas. Aikin da zaiyi yau baima da yawa, dama yanada niyyan zuwa meteorite city don duba lab dinshi dake can gameda yanda abubuwake tafiya na hada maganin CD.

Har yaje ya dawo ba abbas ba dalilinshi. Yaso ya kirashi saidai baiso yayi biyu babu. Ya kirashi kuma bai gama mishi aikinba, shiyasa ya bari saida shi yazo ya nemeshi. Daya ganshi a computer room ya kalla fuskanshi yasan yayi aikin, saiya kwantar da hankalinshi.

Amma yaushe abbas zai barshi yayita jira sai kace wani dan iska ba tareda ya maida mai martaniba. Shiyasa ya turashi task room, manajan akwai sa mutane aiki, koshi kanshi bai tsiraba. Manaja ba ruwanshi inde har akwai aiki, kuma kana wurin, to saika yishi. Dayake yana girmama manajan don dattijone me kwazo wurin aiki da gaskiya.

Zzzzzz, wayar Asiya tayi karan shigowar message ta receiver(chat app nena spiritbook). Mika tayi ta cacumi wayar tanajin gajiya ta kalla. Taga friend request from golden gates. Golden gates? To suwaye golden gates? Hm yanzu haka kawai wani wawane. Ta ajiye wayarta ta mike ta nufa glass balcony.

Aikin masu kwasan gawan de akwai cikas. Kaman basu kwashewa. Ai kamata yayi a kara yawan masu aikin, ta hakane kawai za ayi shi nan da nan a gama. Hm, wazai yarda yayi wannan aiki me hadari haka? Gaskiya sai mai karfin hali. Lallai akwai hadari yawo cikin gawawwakin nan.

Yau kwana biyar kenan da aukuwan wannan annoban, meyasa shugaban kasa baiyi wani abuba da sauri? Ko maganin an kasa samu, kuma mutane sai mutuwa suke. Kullum a news sai taga pickups din gawawwaki ba adadi suna tururuwan kaiwa ramin birnesu.

Kamshin ginger ya bugo hancinta, ta tuna ta jona kettle karami ta wurga danyen ginger ciki su tafasa tare. Da sauri tayi kicin, ya fara tafasa saita kashe. Ta ciro cup daga cupboard ta zuba ruwan ciki ta zuba sugar cokali karami daya ta juya ta ajiye cokalin kan tebur na kicin ta kurba hadiyewanta keda wuya tayi murmushi.

Dawowanta boss office, taga wayanta ya gama haske ya dauke. Ta duba, ah ah! Wai waye wannan golden gates din? Sun sha mata kai da friend request.....wow!!! Wato tun daga receiver, zuwa yellow, thisapp, grammagram, rose petals, sai request suketa turowa da messages. Tayaya ma akayi suke turoda messages ta chat apps dinnan, ai tanasha sai in sunada lambartane zasu iya chatting da ita!? To taya akeyi suke chatting da ita??

Asiya ta saki ajiyan zuci ta fara dubawa. Rose petals: 'Salaam, how are u beautiful?'

Yellow: 'How u doin, precious one'.

Grammagram: 'My noor'.

SB receiver: 'Waiting for ur response, my rose'.

This app: 'Hey babe, looking good'.

LOOKING GOOD!!!? Taya akayi suka san..... ko yasan she's looking good? Aide ba cameras a offices cikin pharmacy din. Sede a reception da waje. Ta amsane ko ta share. Zzzzzz, wayarta ta sake kara, ta duba.

'I know its creepy but I promise u I mean no harm'.

Hankalinta yayi sama ta tsaya tana dube dube ta mike ta fito glass balcony tana kalle kalle ko zata hango wani ko wata koma waye mai yawo da hankalinta.

'Okay, stop this joke'.

Ta amsa ta rose petals.

'Did u feel any joke in my words, beautiful?'

Tayi dan jimmm.

'Tell me who u are'

'The king who'll rule ur hrt'

To! Ji wani kuma, ina ruwan su king, kai mutane can be very funny. Batama sanshiba, bata taba ganinshiba amma ya wani yi bake bake waishi king.

'Oh really, and how do u hope to achieve that?'

'If u give me a chance, baby'.

Lallai wannan ya iya jawo hankalin mutum da kalamanshi. Yeah, masu dadiba. Amma an shata ta warke, duk dadin bakinshi da kwantar da kai bazata karayin kuskuren bada zuciyartaba aje a karyo ba shiri. Maza masu gari, kai mutanen nan a barsu kawai in sunason mace to itace duniyansu, inko kika fita ransu, Allah sarki, bolama ya fiki daraja a wurinsu.

'How did u get my number?'

'Babe, ur number is not a problem'.

Mamaki ya kamata, tasan boye mata yake amma dole akwai yanda akayi ya samo lambar.

'Really, I need u to tell me, or I will drop u'

Haba batason yawoda hankali.

'Whoa! Easy sweety, saw your video on rose petals, since then I couldn't think of anything but that video, I watch it several times and ur thought engulfed every part of me'

'I saw how u pour ur heart in to the video which I derive certain things about u from'

'Hankalinki, kinada hankali mai zurfi da tunani, a lokacin while you are stranded but kina ta kwantarwa da mutane hankali kuma at the same time kina karfafa musu gwiwa'

'Shigarki, ur dressing is amazingly awesome, I despise ladies that expose their bodies in d name of looking attractive. It really disgust me but u, my dear are a diamond in a rough'

'Kalamanki, sunada sanyaya zuciya, and when u listen, you'll think that the epidermic is over bcox it's peaceful, calm and sweet.'

'Imaninki, only mai imanine in this time zai tunada Allah ne mai kawowa da daukewa. Wani in ya rude, sede yace gwamnati batayiba.'

Asiya ta fashe da dariya. Wow lallai wannan yasan yanda zai jawo hankalin mutum kanshi kam.

'Wow! I'm even speechless, all these kayi deriving from the video I made!?'

A gajiye, a azabce, a wahale, Abbas yana zaune idanunshi sunyi ja, yana duba screen na computer. Manaja yana kishingide kan couch yana cin ayaba. Abbas ya kalleshi. "Wai har yanzu bai kira bane?" Manaja ya kalloshi cikin tunani. "Oh aiko tun dazu yayi flashing, na manta ban gayamaba".

Haba, da abbas ya mike fuuuu yayi wuta ya fice cikin bala'in fushi da gajiya. Yanzu haka da ganganne yaki gaya mishi, mtsssw. Ya iso bakin kofan office din hafiz, wayarshi tayi kara. "Waye!"

"Alhamdulillah! alhamdulillah hamdin kaseeran mubarakan, don Allah saurareni abbas, wai, na gode Allah...".

"Who's this?"

"Nine, gadafine".

"Waye gadafi?"

"Gadafi ruma, I really need your help don Allah".

"Where you at?".

"Ina rose city na makale wallahi, a wani shop tareda wasu, Allah ya so basu badamin cutar ba".

"Me kakeyi a rose city? I thought ka dawo tuntuni?"

"This bloody epidermic yayi getting dina stuck a wani unguwa... Miye sunan unguwan nan?...wani minor street. Please abbas can you get me out of here?"

"Well it depends...."

"On what!?"

"Location din da kake. If it is less dangerous, we can send a troupe there to get you out, I make no promises though if it is a restricted area. So we will contact you soon after we check the possibilities."

"Thank you so much abbas, please try harder, nasha wuya wallahi."

Shigowan abbas keda wuya ya kusa cin karo da hafiz. Yayi sauri yaja baya.

"No salaam, poke your face in to my office straight ahead, of course this is bound to happen". Hafiz ya wuceshi zai fice daga office din. Abbas ya dakatar dashi. "I'm sorry sir, handsome wait". Handsome sunan 'yan gidansu hafizne, abbas yake kiranshi hakanan don hafiz bai yarda abbas ya kira shi boss ko sir ba. "Yanzun nan nayi getting call daga ruma, yana rose city, stranded a minor street and seeking assistance."

"Really, mekace mishi?" Hafiz na duba note.

"That we will look into rescue possibilities."

"Good." Hafiz zai wuce, abbas ya kara dakatardashi. "Well?"

"Yeah, go ahead and do your thing." Hafiz nata duba wayanshi yana tafiya.

"Do you want me to come with you". Hafiz ya dan kalleshi ya wuceshi tareda mika mishi note dinshi. "I don't think you are fit for that bas, a little late again?"

"Ba laifina bane, manajane ya manta, again". Ya hade gira rai a bace.

"Serves you right". Hafiz ya murmusa ya fice. Eh se kace ba laifinshi bane wannan azaban daya sha.