webnovel

TA ISO

A deadly virus was detected in rose city and kills people within seconds. The government issued a state of emergency until a cure is found. A handsome zillionaire volunteered to find the cure, in the process he met Asiya the gorgeous pharmacist who was stuck in her work place due to the government orders. Love builds between them as the virus kills and threatened to wipe out the entire city. However, the cure brought them closer and then........

Fatimazahra35 · perkotaan
Peringkat tidak cukup
20 Chs

BABI NA SHIDDA WANI AL'AMARI KUMA: MUTANE MASU DAUKE DA RIGAKAFI

"Assalamu alaikum ya jama'an rose city, name's Asiya liman, a pharmacist. I am here in Ahmed pharmacy bold street and i have a story to tell". Asiya na tsaye a balcony me glass na office din Ahmed boss dinsu ta fara video. "Earlier yesterday morning, rose city was engulf in terror, an unknown disease now called cervix disease, emerged into the city of rose, killing a lot of people, men, women and children". Ta daga wayarta sama don aga bayanta.

"All the things you are seeing behind me, are bodies of people who are victims of cervix disease. I am here all alone, waiting for the dust to calm. And I know other people are also stranded like me. Fear not Insha Allah all will be well. My fellow citizens do not lose hope, do not lose faith, we are together in this and Insha Allah we will overcome it".

Anata nunawa a ThisApp, Spiritbook, yellow, grammagram, rose petals(social medias ne da chat apps) da sauran t.v channels.

Kura ta tashi a gefen hanya inda gidaje suke. Budurwa na labe itada karamar yarinya suna kallon kuran, lafawan kuran keda wuya sai sukaga mutumne ketayin birgima a kasa kaman kwari dubu sun lullubeshi sunata cizo. Can sai yabar motsi. Suka kalla juna suka maida kallon gareshi.

"Na goma sha biyu kenan", budurwar tace. "Wannan bai dadeba kaman sauran", yarinyar tace, tana gaban budurwar a labeda katanga suke. "Minti uku kawai, abin na tsananta", budurwar ta duba agogonta. Su biyun nan, wannan budurwa da karamar yarinyarda farouk yaci karo dasu a kantin da yasha ruwa ya gudu. Yanda suke magana da gani sunyita ganin abubuwan tashin hankalin da yanzu zuciyarsu tayi tauri, tsoron ya fice.

Budurwar ta kara duba agogonta. "Muje, sun kusa zuwa".

"Ni yunwa nakeji". Karamar yarinya ta kalla budurwan.

"Muje to". Budurwan ta wuce, yarinyar tabi bayanta.

ISOLATION CENTRE #10

Likitoci su uku suna tsaye bakin kofan quarantine room suna tattaunawa, suna kallon quarantine room. "ka tabbatar matan is positive?", Likitan mace ta tambaya.

"Of course why else zan sata a quarantine room. CD(cervix disease) ya kashe mijinta. Tace shi mijin nata chemist ne, sunanshi mansoor. Ya bude chemist a gaban gidansu, kuma she was in contact with him kafin ya mutu". Likita namiji yayi bayani. "Itace fa wadda team din abdulaziz suka ce sun ganta tanata kuka a hanya da sukaje neman fresh sample, tana a taimaketa mijinta ya mutu, shine suka tambayeta address din gidanta ita kuma suka kawota nan", likita mace tayi bayani.

"She is immune(mai rigakafi a jini). We could use her, muje mu sanarda director jinin ta zaiyi amfani". Likita na uku yace. Ashe duk surutunsu matar mansoor dake dakin kebewa wato quarantine tana jinsu.

Wucewarsu keda wuya ta fito sanye da hijab da nikaf ta lallaba har ta kai gate din fita isolation center. Mai gadi na tsaye wurin shi kadai, ta jujjuya tana kalle kalle can taga dutse ta dauka ta gefa wani wuri, dataga bai juyaba ta sake daukan wani dutse ta gefa sai hankalinshi ya kai ga wurin yabi yaga meke faruwa, ta sulale ta gudu.

Gudu tayita yi harta isa wani unguwa, shiru kakeji ko tsuntsu ba a jin kara. Tana mamaki tana tafiya sai ji tayi karan dariya, ta jujjuya bataga kowa ba ta ruga wani gida ta fake.

Samari uku suka fito rikeda makamai, suna cika suna batsewa.

"Kashe mu suke so suyi, suce bazamu fita neman abinciba kuma su basu tanadan manaba", siririn saurayin yana tafiya rikeda lauje kaman laujenne ke janshi. "Wallahi basu isaba", kakkarfan saurayin ya daga takobi sama yana ihu.

Wani karamin yaro ya ballo da gudu yana a taimakeshi sun mutu sai kawai ya sankare a tsaye ya fara kaki, kaman abu ya tsarke mai a wuya. Samarin uku suka sankare suna kallonshi, yaron ya fadi kasa ya rike wuya ya fara birgima yana tada kura can ya bar motsi. Hankalin samarin ya bala'in tashi suka fara jada baya, wani iska ya taso daga gefen gawan yaron yayo kansu ya bada musu kura ya wuce wurin matar mansoor dake boye ya bada mata kura ya tafi.

Kuran na lafawa sai kakkarfan saurayi yaga siririn yanata birgima kusa dashi. Idanunshi suka zaro yanaja da baya. "Musa! Musa!! Mush... Mush...". Ya rike wuyanshi, dubbb ya fadi ya hau birgima. Na ukun samarin na ganin haka haba, kafa me naci ban bakiba. Ya ruga kenan saiyaci burki ya rike wuya yana kaki, dubbb shi ma ya fadi sai birgima dukansu suka bar motsi.

Matar na ganin haka itama ta arta a guje a rikice. Ta iso wani unguwa taga gawawwaki birjik. Gaba da ita ta hango kura, kuran na lafawa sai taga mutumne can sai yabar motsi. Haka taga har mutane uku sun mutu. Tuni tayi kwana ta bar wurin tana mamakin wannan abu. Tayi gudu harta ga kanta cikin wani gida, koya akayi tazo? Oho. Gajiya ya bade jikinta ta zube jikin bango, idanunta sunyi nauyi se bacci.

Masu kula da kare cututtuka ta kasa wato NDCC, sunyita kokarin ganin sun samu maganin cervix disease, har hada hannu sukayi da wasu kamfanonin binciken cututtuka mai zaman kansu amma abin yaci tura. Wani al'amari Kuma shine, cutar ta sake rikida(mutation). Da tana daukan tsawon mintuna 10 a jikin mutum kafin ya mutu amma yanzu mintuna uku zuwa biyarne depending on karfin jinin mutum.

Al'amari na biyu kuma shine, dama Allah baya toshe duka kofofi ya bar mutum cikin zullumi. Se wasu mutane jikinsu ya zama baya nuna alamar cutar, kuma cutar bata illah a garesu. Dukda haka tana jikinsu, zasu iya badawa wasu amma jininsu za a iya amfani dashi wurin magance cutar.

Inda NDCC zata samu mutanen masu rigakafin, da ciwon kan baiyi tsananin hakaba. Yanzu cutar basai an sha maganinda bazai magance taba take hari, karfi take karawa na karan kanta.

Cutar Idan ta shiga jikin dan adam ta samu yanda takeso saita fara girma da yaduwa a cikin makogoron. Tana cin abinci daga jikin mutum tana kara karfi tana rikidewa. Shiyasa cikin mintoci kadan cutar ke kashe mutum.

Amma akwai wata sinadari a cikin jinin mutane masu dauke da rigakafi. Inda likitoci zasu samu mutum ko dayane mai immunity(mutum mai rigakafi), zasu iya hada maganin CD, a hakan, komai bai zuwa da sauki.

Praises farouk yasha daga wurin asiya don taga video datayi ta tura mai, yayi editing yayi kyau. Yanzu kowa yasan inda take, halinda take ciki.

'Wai meya samu abokanka 😀, ka kirasu kuwa?'

Zaune a balcony na office din boss tana chatting.

'Muhsin na gidansu, faisal yana gidan budurwanshi'.

'Whaaaat! 🤣 ya akayi ya karashe a can?'

'Gudunshi ya kaishi wurin😂😂, aina mishi dariya kaman me. Zak's Kuma yana wani unguwa stranded just like u, but he's safe'.

'Eyya, been stranded ba dadi gaskiya koda I have whateva I need here but...'.

Motsi ta gani a karamin gate, ta mike tsaye tana kara kallon abinda idanunta ke nuna mata. Wani tsohone yazo jikin karamin gate na pharmacy ta gefen main gate, yana kokarin bude kwadon data datse yayi ya kasa, ta zuba mishi idanu cikin mamaki. Can ya rike wuya ya makale da kofan yanata girgidi daga baya taga ya bar motsi.

Kirjinta na bugawa taja baya ta manne da kofan glass na balcony. Karan shigar message ya dawo da hankalinta ga wayan.

'Sis, lafiya?'

'Whts goin on?'

'Sis ya naji kinyi Shiru?'

Da sauri ta goge sakonda ta rubuta ta sake wani.

'Hmm, na gajine, zanje in dan kwanta'.

Tura message keda wuya ta zura wayan aljihunta. Cikin sauri ta dauka face mask da hand gloves tasa tabi stairs tayi kasa, taje kofan baya na cikin pharmacy ta cire sakata tasa hannunta kan handle din bude kofan ta dakata.

Hannunta na rawa, ta hura iska ta mask cikin fargaba, tana jin bugun zuciyarta a kunnuwanta, tayi addu'a ta bude a hankali ta leka waje ba kowa ta wurin, ta fito daga ciki ta rufe. A hankali ta fara zagayawa zuwa main gate, isarta keda wuya taga lallai mutumne tsoho zai kai kimanin shekaru 70 koma yafi, makale jikin karamin kofa.

Ta kasa motsi ta tsaya ta zuba mishi ido. Toya zatayi? Don dai tsohon ya mutu. Inta barshi a wurin, batasan lokacinda za a kwashe gawanshiba. Kuma bata son ta dinga ganinshi kullum. Taga icce a kasan bishiyan dake cikin pharmacy, tunani yazo mata.

Tsaye take a gaban kofan rikeda icce da sanitizer na spray. Jikinta gabaki daya rawa yakeyi. Abinda wahala, ta matso kusa ta lura da yanda ya sagayo hannunshi cikin karafen gate din, shiyasa bai fadiba duk girgidin da taga yayi.

Sa iccen tayi ta baro hannunshi da kyar, har ya fara kamewa. Kirjinta na bugun babban mandiri. Badau badau badau! Tayita baro hannun da iccen da kyar ta samu ya fara zarewa. Ta dan kara tura hannun se kawai ya sulale ya fadi dippp a kasa. Zufa ya gangaro daga goshin asiya, tayi sauri ta fesa spray. Sai kawai iska ya taso daukeda kura ya bade asiya.