webnovel

TA ISO

A deadly virus was detected in rose city and kills people within seconds. The government issued a state of emergency until a cure is found. A handsome zillionaire volunteered to find the cure, in the process he met Asiya the gorgeous pharmacist who was stuck in her work place due to the government orders. Love builds between them as the virus kills and threatened to wipe out the entire city. However, the cure brought them closer and then........

Fatimazahra35 · perkotaan
Peringkat tidak cukup
20 Chs

BABI NA SHIDA NEMAN DAUKI

Surutun t.v neya tashi asiya daga bacci, idanunta kar kanshi. Tayi mika tareda gode Allah, tama yi latin sallah saboda gajiya ta dauro alwala tayi sallah tayi azkaar. Jawo wayanta tayi ta duba time, 7am. Yunkurawa tayita tashi tana shafa cikinta. Kitchen ta shiga ta bude drawer ta dauka pan ta ajiye kan cooker, ta bude fridge tana tunanin abinda zataci.

Zaune take a couch tana kallon news tana cin vegetable indomie da fried egg, mountain dew na ajiye a gefe. Gwamnatin rose city tana neman gwamnatin tarayyan album country data kawo dauki ma rose city don ganin an magance cutar cervix gabaki daya.

Wani outside city channel mai suna badaboom, sunata magana akan yanda aka fara kwashe gawawwakin rose city, suna tunanin if it is safe yanda ake daukan gawawwakin zuwa wurin birnesu saboda duk da mutanen masu daukeda cutan sun mutu, bai hana wasu kamuwa da itaba suma su mutu. Tunda airborne ne hadarine babba yawoda gawawwakin dukda an tanada spray na kashe kwayoyin cututtuka tunda dai ba maganin cutar cervix din bane. Cutar tafi illa idan ta shiga jikin mutum.

Likitoci na bayanin yanda cutan ke gudana a jikin dan adam. Asiya ta dakatarda cin abinci ta bada hankalinta wurin saurare. Ita dai cutar cervix a iska ake shakanta, muddin ta shiga cikin mutum zatayi tafiyane ta tsaya a makoshi ta rike tsoka da jijiyoyin wuya ta fara gina gidanta tana fadadashi. Gada take hadawa a makoshi me kaurin dake sanadiyan suki da toshe wuyan mutum. A cikin mintuna shida da shiganta take rikida ta kara karfi, to muddin mutum yasha maganin da bazai kashe cutar ba kara karfafata yakeyi.

What!!! Asiya ta saki baki, ta tura indomie gefe. Kirjinta ya fara bugawa. A halin yanzu, ba gwamnatiba kawai harda private organizations sun sa hannu don samo maganin cutar amma abu ya faskara. Shiyasa ake neman shugaban kasan album ya agaza donko in aka kasa maganceta, zata iya fita ta bazu ko'ina.

"It is sad to watch my fellow country people die in vain. It's horrible to know how they die in pain. But hakan bazaisa muyi kasa a gwiwaba se munga karshen cutar bi izininillah. I wasn't in the country lokacinda epidermic din ya fara. On behalf of the golden gates corp, we are given out a mass assistance in food, medicine and controlling the borders of rose city against emigration. I am Hafiz Mahmoud handsome and this is how i serve my country. My fellow billionaires, what is your contribution?"

Hafiz Mahmoud handsome, of course ba billionaire bane but zillionaire wanda ke zaune a dazzling city. Kasancewa rose city na daya daga cikin jihohin album country mai daukeda manya manyan mutane, manyan kamfanoni da masana'antu, shine kusada babban birnin tarayya, dazzling city.

An kirasu da handsome saboda kyawawane daga matansu har mazan. Arziki kaman daga bishiya yake a gidansu sede su tsinka. Allah ya albarkaci hannunsu da duk abinda suka taba seya zama zinari ko lu'u lu'u. Ko rabewa kayi dasu zaka samu naka, sunan wani gari. Dan da ba a haifabama nada nashi kason dukiya don tsananin albarkanta da yawa.

Golden gates corps computer company ne wanda ya bullo da sabon salona kimiyya da fasaha, sunada branches all over album and worldwide. Hafiz ya ginashi tun yana tashen samartaka, da yake ya taso shi kadaine namiji a gidansu, hakan baisa ya sangarceba, a'a duk abinda ya mallaka aiki yayi ya samu bai dogara da dukiyan mahaifinshiba duk da komai na kan tiren silver sede kawai ya dauka. Ya san zafin neman na kanshi, ba raggo bane.

Bai tsaya a kimiyya da fasahaba kawai, ya hadasu da kamfanonin mota, jirgin sama, kasa dana ruwa. Ta hakan ake hadasu tareda sabon salon(innovation). Misali suna hada mota mai tuka kanta, direba sede ya linke hannaye yana kallo, ko bike(mashin) mai aikida wutan lantarki daidai sauransu. Labarinsu, handsomes ba boyayye bane, kana hawa yanar gizo zaka gani, sede in basu ga daman a ganiba, komin maitarka dole ka hakura. Ba abin mamaki bane donya agaza, kudi ba matsalanshi bane.

Oh, kowa se kawo dauki yakeyi ma rose city, don an gane da cewa inta fa durkushe, to kowama ya durkushe. Asiya ta murmusa tanata kallon kyakkyawan fuskan Hafiz, can ta girgiza kanta. Waya sani koma budurwarshi ba a kasan takeba. Sanin 'yan gidansune da son auren bare.

Asiya ta dauka wayanta ta jawo jakanta ta ciro charger ta jona wayan. News ake kwararowa na masu bada tallafi, tunda Hafiz ya bude fage shikenan masu hannu da shuni suka dinga fitowa kodanma ace sunyi. Asiya ta shishina jikinta, wanka takeson tayi sede babu kayan chanji. Ta kallo hijab dinta ta sura ta wuce toilet na kasa.

Jikinta lullube da hijab daga sama har kasa taje kantan magani ta samo man shafawa a jiki na dermatologist, ta shafa, tasa face mask ta dauka bucket ta fita ta kofan pharmacy na baya ta hau stairs zuwa karamin balcony ta shanya under wears da uniform dinta, ta koma kitchen tana wanke kayan da tayi girkida.

GOLDEN LABORATORIES

Helicopter ya sauka a filin saukanshi a saman building din golden laboratories, sunan lab din makale a jikin building din rubuce da kalan gold da baki. Kofan helicopter ta bude, kafa sanye da burgundy bakake, brioni black jeans da sunspel shirt me dan karamin hannu wanda ya nuna kakkauran arms dinshi. Agogon rolex daure a kakkauran hannunshi, shady black sunglass na Nathalia chantal makale a idanunshi ya zauna kan dogon hancinshi, kunnenshi makale da iPhone 11 Pro Max yana magana. Tsaye a gefenshi na hannun damanshine Abbas. Ya mika ma Abbas wayan suka shige cikin building din.

Hafiz yazo lab dinshi domin yaji in an samu cigaba akan maganin da ake hadawa na cutar cervix. Ya riga ya dauka alkawarin zai taimaka da magani shiyasa ya tsanantama duk laboratories dinshi around the globe don su bada himma wurin ganin an hada maganin da wuri.

Daga gani dai ba aci nasaraba bayan gwaje gwajen da akayi tayi a lab din. Tsaye yana rikeda sunglasses a hannu yana kallo ta glass din lab, ma'aikatan lab suna fitarda gawawwakin lab rat(beran lab). Ya maida glass dinshi a idanu, ya juya tareda Abbas suka fita daga building din.

Hamshakan jeep SUV bakake guda biyu ne pake a gaban building. Zagaye da jeeps din bodyguards ne tsaye. Hafiz ya doso tareda abbas da likitoci biyu, budurwa da dattijon namiji. Yana isowa ya taka birki, ya juyo yana fuskantar likitocin. "Contact me as soon as the antidote is ready, have you gotten all you needed to conduct the experiment?". Ya juyo ga likitan namiji cikin authority. "Yes sir, everything is ready we just need tim.....". Hafiz ya katseshi. "Time is limited. You have to hit the nail harder, doctor rahim".

Idanun budurwar likita kar akan jikin hafiz, tana kallon yanda shirt dinshi ke nuna arms manya, 8 pack abs dinshi na nunawa ta jikin riganshi. Dago idanunta keda wuya ta sankare, oops an kamata tana kallo. Ta cikin shady black glass dinshi ya harbota da kallo mai sa mutum jin tsarguwa dukda bata ganin idanunshi sosai ta shiga taitayinta ta sauke idanunta kasa.

Hafiz ya juya yana tafiya yana magana da Abbas. "Abbas, call the grassland lab for any update, then set a meeting with tahir and the gates executives in 2hours". Direban dake tsaye gefen motan ya bude ma hafiz kofan baya, hafiz ya shige direban ya kulle, bodyguards suka shige dayan motan. Abbas yanata latsa note (computer) ya bude gefen pasinja ya zauna ya cigabada tabe tabenshi. Motocin suka sha kwana suka bar haraban wurin.

Daga nesa za a iya ganin fararen kaya iska na kadasu da alamun sun bushe. Asiya tasa mask ta daukosu ta dawo ta cire mask tasa kayan a jikinta. Zaman kadaici ya fara isanta ta dauko wayarta tana chatting da kaninta.

'Sis, kiyi video na zamanki a pharmacy din, you can even take pictures around you ki turo min'.

'Kayime dashi?'.

'Kede kiyi sis, it'll be fun da zama baki yin komai'.

'Gashi ina chatting dakai'.

'Come on sis'. Ta saki ajiyan zuci, ta cigabada typing.

'Okay rouk, how does it goes?'

Hotontane ke motsi cikin wayarta tana yin video. "Assalamu alaikum ya jama'an rose city, name's Asiya liman. I am here in Ahmed pharmacy bold street and i have a story to tell".

Farouk na kwance akan kujera yana tattaba waya, ya gama ya murmusa.

"Please how soon can you get the work done? What do u mean by that? There has to be a way...what curfew!...no no no no.... I'll contact him". Ahmed ya Katse wayan. Yana zaune a balcony na gidanshi, ya fara taba waya. "Honey, look". Yusrah ta iso cikin hanzari ta zauna gefen Ahmed tana nuna mishi wayanta.

Babban Asiya ya shigo dakin mom cikin hanzari ya dauka remote ya kunna t.v, channel din amazing world. Mom na kwance ta dago da sauri ta jawo jiki bakin gado, dad ya zauna bakin gadon suka kurama t.v idanu.

"Handsome, look at this video". Suna zaune cikin mota Abbas ya mikoma hafiz iPad ya diba. Motocin suka tsaya a cikin haraban golden gates corp, main branch a dazzling city yake, a rumfar shiga building din motar dasu hafiz ke ciki tayi parking, escort dinshi suka wuce garage. Abbas ya fito daga motan, direba yayi sauri ya budema hafiz ya fito, Abbas ya tsaya gefenshi suna kallon video din tare a rose petals(social media ne).