webnovel

TA ISO

A deadly virus was detected in rose city and kills people within seconds. The government issued a state of emergency until a cure is found. A handsome zillionaire volunteered to find the cure, in the process he met Asiya the gorgeous pharmacist who was stuck in her work place due to the government orders. Love builds between them as the virus kills and threatened to wipe out the entire city. However, the cure brought them closer and then........

Fatimazahra35 · perkotaan
Peringkat tidak cukup
20 Chs

BABI NA SHA SHIDA HADUWA 2

Safiya ta waye a garin rose, Ahmed pharmacy. Kyawawan idanun Asiya suka bude, ta kalla gefenta taga ummi, ashe ba mafarki bane. Lallai kowa yazo, hardashi, ta lumshesu tareda murmushin farinciki.

"Ke kin ma yi bacci kuwa? Don harnayi bacci naga kina ta duba waya, hala chatting kikayi?"

Mika Asiya tayi ta rungumo throw pilo tana murmushi. Jiya kam da kyar ta iya bacci don zuciyarta na kasa, wani madaran soyayya takeji yana kwararowa cikin zuciyarta, ta mike zumbur. Hulan kanta ya sulale daga kan, dogon bakin gashinta mai laushi ya bayyana, ta dunkuleshi ya tulu a baya, ta shiga bayi ta gama abubuwanta ta fito.

"Kuma kince baki taba yin retouching ba? gashin nan naki?"

"I don't need that. On its own yanada sulbi inko nayi aiko kitso dayan da nakeyi bazai yiba. Muje kicin mu hadama mutane breakfast".

"Ko ki hadama mai gidaba". Asiya ta hararo ummi cikin wasa, sukayi dariya suka wuce kicin. Suna isa kicin sukaji motsi a ciki, wani kamshi ya bugi hancinsu, suka kalla juna. Asiya ta duba agogonta karfe 8 da minti biyar, to waye a kicin din yake girki? Shigan su keda wuya me zasu gani?

Dishes iri iri ajiye akan tebur dake tsakiyan kicin. Vegetable egg fried rice, roasted sesame chicken, corn flakes da madara, iyye hadda roasted steak(gasasshen nama), toasted bread da omelette (kwai mai hadi)....

"Sis you are late, I hope kinyi bacci jiya?" Ya ajiye jug na tea akan tebur din. Idanunsu Asiya da ummi suka sauka kan hafiz dake ciro wani abu daga cikin oven, ya ajiye baked potato frittatas akan tebur abbas ya miko mishi ketch up.

"Wai tsaya, duk wadannan girkunan wa yayisu?" Ummi ta nuna plates din kan tebur.

"Babe, me am a tea expert, sauran su sukayi". Ya nuna su hafiz. Haka Asiya ta saki baki, dama hafiz ya iya girki?! Haka ummi ta saki baki, haka farouk ya kira ta babe!

"Good morning love, come take your honorable seat". Hafiz yaja mata kujera ya dasata da kyawawan idanunshi. A hankali ta wuce ta kalleshi ta danyi murmushi ta zauna. Ummi zata zauna farouk yaja mata kujera, ta sankare tana kallonshi yayi mata murmushi, ta wulla idanu taga Asiya na zaune hankalinta na kan hafiz, tayi sauri ta canza kujera ta zauna gefen Asiya, taki zama a kujeran da yaja.

Saime? Farouk yaja kujera gefen ummi ya zauna, ta kara sankarewa inna lillahi! zama yayi kusada ita? Ta saci kallonshi yanata diban abinci abinshi. Hamid ya shigo ya diba abinci ya dauka spoon biyu ya fita. Abbas ya diba abincin shima ya fice. Wato kada a takura musu kowa ya fice.

Ai Asiya tasha irin masu kudinnan saidai ayi musu komai, bata taba zaton wai hafiz karan kanshi ya iya ko yanka albasaba ballema girka wadannan top chef dishes din. Kai cokali daya na frittatas baki saiji tayi mazakutan dandanon bakinta sun taso, bata san lokacinda tace umm ba.

Hafiz ya kalleta yayi murmushi. "Haffy dinki ya haduko?" Ya daga mata gira daya. Ta kada kai tana taci tana murmushi. Ummi ta kurba tea, wani madaran dadi ya sauka bakinta. Farouk ya kalleta. "Tea din ya haduko?" Ta kara sankarewa, yo shi wannan ai saita zama kankara inya cigabada haka. Ta tattara karfi tace, "Yayi, sosai".

Asiya ta mika hannu zata dauka toasted bread, hafiz ya dago mata plate din ta dauka. Ummi ta mika hannu zata dauka plate din steak, farouk ya dauko ya mika mata. Ta kalleshi, murmushi ya sauka a lebbanshi tayi sauri ta karba tareda kauda idanunta daga shi.

Gasa da ogan gasan ai kiran ruwane. Wato yaron nan so yake yaga ya kure hafiz. Murmushi hafiz yayi, baiga laifinshiba amma dole ya tsaya matsayinshi. Baida lokacin kowa inba na princess dinshiba.

Wai farouk ba wasa, harya fara harin ummine haka? Asiya ta kalleshi. To ashema akwai wani abu a zuciyarshi saboda tasan kaninta idan yana son abu baya bata lokaci wurin nunawa. Amma is it smart ya dinga tsokano ma kanshi abinda bazai iyaba? Donta lura duk abinda hafiz yayi mata shima sai yayima ummi.

Ta kalla hafiz yana tauna abincinshi cikin natsuwa da kamala. Ta kalla farouk yana tauna abincinshi cikin, to shima natsuwa da kamala? Shin da gaske farouk na harin ummine kode hafiz? Idanunta suka je kan ummi, tana cin abincinta no worries.

Ai worry din duniya ya dameta saboda wani lokaci sai taji idanu akanta, kuma inta kalla wanda take tunanin shike kallon sai taga ba hakaba. Ummi ta kura ma farouk idanu saita maida kallon ga hafiz. Idanunshi na kan asiya, kome tayi a idonshi. Toooh ga kallon ya dawo, tayi sauri ta kalla farouk, ya tsareta da idanu yanata kallonta har saida ta tsargu ta mike tsaye tsam.

"Ina zaki?", Asiya ta tambaya.

"Um... Na koshi". Ta fice daga kicin. Asiya ta mike ta kalla hafiz. "Abinci yayi dadi, thanks".

"You're welcome sweetheart, amma nema kin kishi?", hafiz yace. "Eh". Ta kalla farouk. "Rouk, a minute please".

Fitarsu wajen kicin Asiya tayi attacking farouk. Kada ya kuskura ya fara abinda bazai iya cigababa, taga yanda yake wasa da hankalin kawarta to tana gargadinshi ya tsaya nan koya haduda fushinta. Taya za ayi tace yana wasa da hankalin ummi, shiga da gaske...

Ummi itace kawarta ta farko after a long time, kuma Asiya bazata yarda farouk yayi wasa da zuciyar taba saboda yana neman kure hafiz. Ta riga ta gaya mai hafiz dabanne amma yaki yarda, inta dalilin haka yayi hurting ummi bazata taba yafe mishiba. Asiya ta juya cikin fushin ta wuce.

Wow! Sis da gaske take? To, ya kira ruwa kenan. Farouk ya rasa meyasa amma yana ganin akwai wani abu tattareda hafiz baisan meyaba amma abin na nan. Koma de meye zai ganone donba wanda zai kara cutar da sis din.....

Juyawanshi keda wuya kirjinshi ya buga. Hafiz ne tsaye yana mishi kallo mai kaifi mai ratsa kwalkwaluwa da jiki da kafafu su sankare mutum ya kasa tafiya. Hafiz nata mishi kallon har yazo ya wuceshi yayi kasa. Siririn zufa ya gangaro daga goshin farouk ya taba yana mamaki. Meyasa yake zufa kaman wani mara gaskiya? Meyasa hafiz ke mishi kallo irin haka kaman yana tuhumarshi da son rabashi da masoyiyarshi? Lallai akwai aiki.

"Now that she's okay yaushe zamu koma handsome?"

"Kai zaka koma da dare na riga nayi arranging komai......"

"And you?"

"Inada aikinda zanyi anan...."

"Seriously?"

"You dare to question me?"

"No ba haka bane...."

"Enough, you'll go tonight by 7:30pm. Kayi contacting major gabriel, number dinshi na a phone dinka."

Ya za ayi ya tafi bayan bai gama ganawada masoyiyarshiba. Ashe a waya somintabine yanzu daya ganta ya tabbatar da cewa Asiya macece, ga tsayi, ga kyau, ga wannan tausayin daya hango, don saime tausayi zai damuda wanda ya tsoratashi don yace bai ci abinciba har kwana uku. Tayako zai tafi ai sai yayi tasiri sosai a cikin zuciyarta.

"How about shahid?"

"What about him?"

Kawai abbas ya gayamishi cewa hafiz ya tafi wani urgent meeting ne a wani gari, sannan yayi making sure wasu kannai basu dame shahid dinba. Dago kai da sauri abbas yayi yana mamakin yanda akeyi hafiz yasan raihana tayi halinta. Hafiz ya wuce ya zauna kan kujeran gaban tebur a office din asiya, yaga hotonta da kayan gida, ya jawo karamin frame din yanata kallo.

Sanye Asiya take da bubu da skirt kampala yellow da baki, iya gwiwanta aka dauka. Ta waigo ta baya tana dariya, dimple dinta ya lotsa sosai. Zai taba gajiya kuwa da kallon this beautiful lady.

"Office fa?"

Sai kace da abbas da tahir bazasu iya handling things kafin ya dawoba, yadai lura abbas baya son barin gefenshi ko kadan. Yafi dason ganin koda yaushe suna tare dai, to wannan karon dole ya hakura, hafiz kam saiya gama abinda ya kawoshi rose city sannan zai koma.

Ba koda yaushe ne ake samun mace kaman asiyaba a barta ba tareda anyi dashen abu mai karfiba. Don har iyayenta dole susan da zamanshi. A'a wallahi bazai iyayin wannan sakacinba wani ya rigashi. Yazo baiyi achieving komai ba saiya koma, no way.

Bukar ya matsa lallai su tafi tunda lafiyan wadda su kazo ceto kalau. Ummi tace itafa ba inda zata sai tareda Asiya, wancan karon ta tafi abinta ita kadai bataji dadiba saboda haka yanzu bajada baya saida Asiya. Farouk ya kwantar musu da hankali baiga dalilin nacewa akan zancenba donshi zai tafi da 'yar uwarshi gidane.

A reception suke suna tattaunawa. Ummi ta kawo zancen ai unguwansu farouk nada nisa, gidansu ummi shi zaifi dacewa aje ya so kowa ya koma gida idan kuran ta lafa. Farouk ya kalla ummi yana tunani.

Tabdi! Gotai gotai dasu sai suje gidan mutane su cika kawai. Farouk dai baison ya zama kaman abokinshi wanda yaje gidansu budurwanshi ya lake can, koyama aka kareshe dashi oho? Shi kam baza ayi wannan kasalandan da shiba.

To ai hadarine ma bin hanyan nan, ummi tacigaba. Ga cuta, ga sojojin, ga kuma masu gwaji. In suka kamasu ai kashinsu ya bushe, kawai..... Shi dai gida zai kai 'yar uwarshi fakat.

"To wanda kuma baida gata fa? Usman, sai in kore shi in rufe wuri in tafi?"

Ai usman ba responsibility din sister dinshi bane...."Ka goya bayan in watsar dashi inda ya fito kenan! Bazan iyaba, ai tunda na amince da yazo ya zauna, ya zama responsibility dina in kula dashi. Bazan iya ce mishi ya komama wahalan daya kawoshi nanba, domin in wani abu ya sameshi to wallahi bazan taba yafema kainaba".

Asiya ta kallo sauran mutanen dake tsaye."We are not humans if we lost our humanity? Son kaide yayi yawa, kowa nan yasan dandanon azaban yunwa idan ta kamashi, ba hankali. Bawan Allan nan bai iya yin maganaba saida ruwa ya taba makoshinshi. Shiyasa Allah yayi hanin horo da yunwa, to idan mukayi haka bamu hore shi da yunwaba".

Asiya ta gane, farouk bafawai yace a koreshi bane. Babban mutumin zai iya kulada kanshi so ba responsibility dinta bane, ita kanta tana karkashin iyayenta kuma zasu so suga 'yarsu ta dawo musu. Of course zata koma amma saita san usman yanada madafa.

To Inba asiyaba ai baza a zauna nan ba har abada, in aka zauna sai abincin ya kare, a fada wani wahala kuma, ummi ta kawo zance. Koma a kira shi usman din a mishi jawabin abin dake faruwa, ya yanke hukuncinshi da kanshi, hamid yayi kari.

Wannan ai forcing dinshine yabar wurin, asiya ta lurar dasu. Ummi ta girgida kai, to barinshi Asiya zatayi a wurin su tafi, ko kuma zata tasashi gabane su tafi? Asiya tace ko daya amma bazata taba yin abinda suke son tayiba. Farouk yayi conclusion, wato dai so take kowa ya zauna anan na tsawon kwanakinda ba asan lokacin tafiya ba ko? To bada shiba wallahi, ita kanta tasata gaba zaiyi su tafi. Ummi tace ba inda zata sai taga Asiya tabar wurin.

Ai sai suyita yi, Asiya ta wuce ta zauna. Ummi tayi ajiyar zuci ta kalla farouk. Ko yaje yama hafiz maganane donshi kadai kila zataji magananshi.

"Wow! Am very impressed, my love gaskiya kin burgeni. You are so selfless to the point of bakijin reasons".

"Gaskiya saidai kayi hakuri hafiz, I can't do this...".

"What about him?" Ya nuna bayanshi da kai, saiga usman ya shigo. Da sauri Asiya ta mike tayi wurinshi. "Usman wani abune ya taso kuma..."

"Aiiiii ina sane."

"Eh?!"

"Naji komai, ba damuwa kinyi kokarin ai, kin taimakawa rayuwata godiya mai tarin yawa madam kuma karki damu dani ina tareda oga." Usman ya kalla hafiz. Asiya tabishi da ido.

"When abbas go home tonight he'll be taking him along to dazzle, baida kowa nan garin, a can kuwa a whole life is awaiting him."

"You did this for him?!"

"I did this for you my dear."

"Alhamdulillahi nagodewa Allah daya kawo muna mafita, da bansan yanda za ayi da wannan Asiya mai taurin kanba". Ummi tace.

"Ai in sis ta dage akan abu to saidai kowa ya hakura."

Ita kadai tasan halinda ta ganshi lokacinda yazo kaman wani mahaukaci ya firgice ga kishi ga yunwa. Sannan kuma tace ya koma? No way.

GADAFI

Wannan wace irin masiface, tunda ya fita neman abinci ko ruwa digo bai samuba, ga faty ta lake mishi yau taki zama a shagon. Dole yazo da ita, yarinya tasha mai kai gashi ba ta yarda da kowa saishi. Asalima shiya tsani yara, abu kadan sunyi kuka, abinda ma yafi bashi haushi kenan. Allah ma yasoshi faty bata cika kukaba amma akwai makale mutum.

Gashi yanzu tare suke shan wuyan. Ya kalleta tana tafiya kaman zata fadi. Tunda suka fara tafiya bayan 'yan mintuna kadan saita daga hannu, ya dauketa kenan. Ya yita daukanta har hannayenshi suka sage, yanzu kam bazai iyaba shiyasa dazu data mika mai hannu da gangan ya dauketa ya sake ta subuto yayi sauri ya kamota kafinta kai kasa.

Harta rufe idanu ta kwala ihu don har taga kanta ya fashe don tanan ta sullubo. Saiji tayi an cafkota yayi sauri ya ajiyeta yana ce mata hannunshi sun gaji. Dole ta hakura tayita tafiya a gajiye. 'Yar nema ai yayi maganinta gobe baza ta kara binshiba.

Sai wata dibara ta fado mishi, murmushin mugunta ya sauka a lebenshi. Ba karamin dadi wannan dibara tayi maiba. Dibaran ko itace, ya nema wani wuri su huta in faty tayi bacci ya sulale ya gudu ya barta. Dama yarinyar akwai iya bacci. Wallahi shikenan ya huta da Allah kakai.

Gama yanke shawaran keda wuya sai yaga wani shagon drinks kofan a balle gefen wani gida. Murmushi ya sauka a lebenshi, perfect abandoning spot kenan. Sauri yayi ya dauketa ya dosa wurin. Shiganshi kantin kai tsaye ya hau nema ruwa babu komai, can daga lungu ya hango roban juice.

Balle kan roban juice din yayi ya kurba kadan, faty tayita mika hannu tana yabata. Ya mika mata ta kafa kai tasha tayi nak, ta shanye komai harda karkadewa da lekawa da sudewa. Idanunta suka fara lumshewa. Yawwa daidai kenan, suka zauna cikin shagon a takure donba fili sosai.

Duk wannan bai dame gadafiba domin burinshi ya kusa cika. Faty tana gefenshi zaune sai kawai ta langwabe ta fara bacci. Saida ya bari baccin yayi dan nisa sannan ya dagota daga jikinshi a hankali ya kwantar da ita. Yana murna zai gudu kawai saiji yayi an rikeshi.

Sankarewa yayi a hankali ya kalla baya, hannuntane ke rikeda da haban rigarshi, ta mishi kamun gaske kuma. Duk yanda yayi ya cire hannun ba tareda yayi motsi da yawaba abu ya gagara.

Haushi ya kamashi, bala'yar'iyar yarinya kaman tasan yana neman rabuwa da ita. Gadafi ya rasa yanda zaiyi, ya kalla jikinshi ya tuna akwai singlet dinshi a ciki amma yana kokonton cire rigan saboda akwai rana sosai a waje.

Matar mansoor dai gudu ya kare, a baje take cikin wani gida tayi daddaya da kafafunta da suka kumbura don azaban gudu. Yanzu kam ta kai karshe, inma kamata sojojin zasuyi saidai su kama. Kayan jikinta sunyi butubutu da kura daman dogon bakin abayace da pink hijab. Kalan hijab din ma ya tashi daga pink ya zama brown don datti.

Ba sallah ba salati sai gudun rai. Ba ci ba sha saidai gudun rai. Ba hutu ba bacci, gudun de ranne dai. Wannan ai ba rayuwa bace, kawai dai ba mutuwa bane. Yanzu haka ko motsi ta kasayi saboda kafafun sun sundule. Bari ta rufe ido ta danyi bacci kila kafin ta tashi sun dan sauka.

Motsi taji ta bude idanu ta wulla su zuwa windo, kai!!! Anya mutanen nan mutanene kuwa? Wanne irin jarabane wannan? Ta shiga uku ita shamsiyya. Da kyar ta rarrafa ta isa windo ta leka. Ranta sai daya mugun baci data hango sergeant. Da wani Idanunshi kaman angulu yana kalle kalle.

To sai a cigabada kawai da aiki. Hakanan ta gurfana ta tashi tana dingishi. Amma wannan karon saita canza salon guduwan. A bayan ta gudun musu, saita boye sosai a gidan cikin kushin dinda ya barke, ta shige ta lakume ta kanannade ciki, ta rufe yagan don kar wasu su shigo su hangota, idanunta sukayi nauyi.

Sergeant da team dinshi sukayita neman shamsiyya amma battt ta bace bata. Sun kai awa biyu suna sintiri babu alamanta. Haka nan suka hakura suka tafi. Wannan karan tayi nasaran kubuce musu.

Bude ido tayi saboda karanda taji taga wayam, hankalinta ya tashi ta waiga hagu da dama ba uncle ba alamanshi. Faty ta mike tsaye taga riganshi makale a hannunta ta dauka ta fito daga kantin, rana ta kwalo a kanta, ta fara tafiya tana son tayi kuka tanata kalle kalle ko zataga uncle. Tana karya wani kwana ta taka birki, motocin sojoji suka wuce tareda tada kura.

Labe jikin gini tanata kallonsu har sukayi nisa, zata fara tafiya kenan ta hango mutum da singlet yana fitowa daga dustbin babba, ya sunsuna jikinshi ya yamutse fuska. La! Ga uncle. Habawa da gudu ta arta tayi wurinshi cikeda murna.

Garam gadafi yaji anyi karoda kafafunshi kananan hannaye suka rungumoshi. Ya sankare yana mamaki ya kalla faty, ta dago tareda mishi murmushi. "Uncle na kamaka, mu sake yin wasan". Lallaima yarinyarnan, ita a zatonta wasane yake mata? Gadafi ya zaro rigarshi dake dunkule a hannunta ya bubbuga ta mike yasa. Wasa kike so ko? Zaki samu. Murmushin mugunta ya sauka a lebenshi. Dibara ta biyu ta hadu.

* * * *

Fitan gadafi daga kantin da sauri ya wuce yabi wata kwana, can ya lafto a guje ya dawo ya tsaya tsakiyan hanya yana kalle kalle, saiya hango katoton bola, aiko da gudu yaje ya fada ciki. Ashe sojoji ya gani sun harbe wani sai ga mai gwaji yazo yanama wanda aka harbe wani abu.

Kafin su hangoshi ya koma da gudu ya fada bola. Warindake tashi a bolan nan kaman yayi amai, ga wasu abu masu yauki da sulbi yana cudanya dasu, amma hakanan ya hakura yayita fakewa. Wai meya tsayarda abbas ne ko sun samu delay ne ko kuma unguwan restricted ne? Ai yaci ace ya turo by now haba, ya gaji da wannan azaban. Ya ji motoci suna wucewa har sukayi nisa sannan ya fito. Ya sunsuna jikinshi yana jin haushi yanayinda ya samu kanshi, wai yau shi gadafi rumane har a cikin bola!

* * * *

Gadafi ya kalla faty tanata murna zasuyi wasa itada uncle. Shi kuma yana murna zai rabuda masifa. Yaja hannunta suka shiga wata unguwa ya nuna mata wani gida yace taje ta shiga ta boye shi kuma zaizo nemanta. Ashema akwai hanyoyin rabuwada wannan jaraban bai saniba. Yace tayi maza taje ta boye kuma karta yarda yaganta inba hakaba ya cinye wasan.

'Yan kananan kafafunta suka cilla a guje ta shige gidan daya nuna mata. Ko'ina bude yake, ta shiga palo tana kalle kalle neman inda zata boye. Ta ruga bayan kushin ta boye sai gani tayi kushin na motsi, a firgice taja baya tanata kallon ikon Allah, Idanunta suka fito ta rafka ihu.

Dariya mugunta ya fashe da yana murna yana gudu. Allah ya rabashi da wannan rigimarmiyar yarinya. Ko shifa yanzu ya samu yaji sakat ya....cukusss, ya fada rami a gefen wata mota dake dash road.

"Yi shiru yarinya, bar ihu kar suji suzo su kamamu". Faty tayi shiru tanata kallon wata mata ta fito daga kushin. Shamsiyya tayi murmushin karfin hali, ta fito daga kushin ta zauna a kasa ta kalla faty. "Ya sunanki?" Faty ta juya ta balla a guje tabar gidan.

Tun lokacinda shamsiyya ta fara guje gujenta ta dade bata haduda wasu mutaneba inba wadannan fitinannun sojojin ba. Yarinya a wuri irin haka! Ai gwara taje ta nemota karta fada wata halaka. To ita kadaice ko tareda wani take? Shamsiyya ta mike da kyar ta kalla kafafunta sun dan sauka daga kunburin da sukayi, ta leka taga ba sojoji ta fice daga gidan.

Hango faty tayi tanata artawa da gudu tana kiran uncle. oh yarinyarnan zata jawa kanta harbi inta haduda jarababbun sojojin nan. Ta bita da sauri tana dingishi har suka karya kwana suka shiga dash road. Shigan shamsiyya dash road keda wuya sai ganin tayi yarinyar tsaye tanata kallon kasanta. Bin inda Idanunta ke kallo tayi sai taga mutum rabin jikinshi ya makale a cikin rami.

"Faty!!! yawwa fatyn uncle, zoki fidda uncle daga ramin nan kinji". Faty ta kama hannunshi ta fara ja. Tabdi! Shamsiyya ta lura ai saidaima ya jawo yarinyar duk su lunkuma cikin ramin. Ta iso ta tsaya gabansu. Gadafi ya kalleta yana mamakin yanda akayi ta iso wurin.

"Wa...cece ke?"

"Sunana shamsiyya, bazata iya jawokaba, kai waye?"

"Uncle...dintane, gadafi su....nana".

"Zan jawo dayan hannunka saika turo jikinka daga kasa". Shamsiyya ta damka dayan hannunshi taja, sukayita ja har suka jawoshi daga ramin. Ya baje a kasa yana murna, shamsiyya ta zauna tana nishi, faty tazo ta rungume gadafi. Shamsiyya tayita kallonsu canta mike tsaye.

"Gwara mubar wurin nan domin...".

"Ke dawa?"

"Daku mana, sojoji yawo sukeyi mu shiga wani gida mu kubuta daga sharrinsu". Gadafi ya tashi zaune yana hamdala. Ya godema shamsiyya sannan suka bar wurin suka shige wani gida.