webnovel

TA ISO

A deadly virus was detected in rose city and kills people within seconds. The government issued a state of emergency until a cure is found. A handsome zillionaire volunteered to find the cure, in the process he met Asiya the gorgeous pharmacist who was stuck in her work place due to the government orders. Love builds between them as the virus kills and threatened to wipe out the entire city. However, the cure brought them closer and then........

Fatimazahra35 · perkotaan
Peringkat tidak cukup
20 Chs

BABI NA SHA HUDU BAYYANA 2

* * * *

Wurin bukin ya kayata, hall ne babba na gani na fada, ansa decorations sai walkiya ko'ina keyi. Motoci guda uku suka tsaya daidai shiga hall din. Mota ta farko bodyguards ne, suka fito suka wuce wurin mota ta uku. Abbas ya fito daga gaban mota na biyu, ya bude kofar bayan motan. Hafiz ya fito ya kalla gefe, yaga bodyguards sun budema sisters dinshi kofofin mota na uku, raihana da sauran sisters dinta suka hadu, gaba daya suka shige hall din. Raihana tazo wucewa ta kyafta ma abbas ido tareda murmushi ta shige hall. Abbas ya danyi jim sannan ya shiga hall din.

Tun shigowansu hall din abbas yaga ta kanshi domin raihana tasashi gaba. Kujeranta na gefenshi saita zuro kafarta ta ingizoshi inya kallota tayi murmushi. Har canza seat yayi amma inaaa bai tsiraba don biyoshi tayi ta kora na gefenshi ta zauna. Abbas ya rasa yanda zaiyi da ita ya tashi ya bar hall din tareda cema handsome zaiyi wayane.

Fitanshi waje keda wuya ya jiyo muryarta a bayanshi. Kash! ta biyo. Zadai ayita da gwajewa, badai dole. Da karfi ya juyo ya linkeda hannayenshi a kirji yana kallonta. Ta iso tana kararraya da shagwaba waiya tafi ya barta, sai kace wani mijinta.

To bari taji da kyau daga bakinshi yace mata, from today onwards karta sake damunshi don shiba mate dinta bane. Ba saurayinta bane, haka zalika ba mijinta bane. Inta sake binshi zai mata rashin mutuncin, dama ganin girman handsome ne kuma tana a matsayin kanwarshi shiyasa yake raga mata. Amma yanzu ya gaji wallahi. Badai shi kadaine namijiba da zata sake duka maitanta akai. Ta rabu dashi ya sakata ya wala.

Gama magananshi keda wuya ya juya ya koma hall din. Kirjinta na bugawa, hannunta na rawa saboda takaicin cin mutuncin da abbas yayi mata. Ina laifin wadda tace tana sonka? Wai ita abbas zaima wannan cin mutuncin. Tana cika tana batsewa, ta juya ta bar hall din.

"Pleeeeease bro, kowa yaki jina". Raihana turo baki cikin shagwaba. Abbas na gefe zaune yanata taba note, yanajinsu amma yayi kaman bayaji. "Ina zaki da saidani zakije wurin?"

"Park nefa ni kuma banason bodyguard kuma dad yace dolene su dinga bina, kuma in suna bina samari guduna sukeyi.....".

"Whoa, me ya kawo labarin samari kuma?"

"Saboda wata rana dole nayi aure ai bro".

"Kuma yaune ranan"

"Broooo".

"Fine. Abbas come take her to...where ever she wants to go".

Badan hafiz najida raihana ba da wallahi ya jibgeta a hanya. Don tunda ta shiga motan abbas ta kame a baya waya take tayi da kawayenta, tana gaya mishi magana ta hakan.

"Hmm kede bari, wasu mazan kaman makafi suke". Ta kalla abbas ta rear view mirror, yana sane yaki kallonta yanata tuki abinshi.

"Haba hahhh ai har miss world ma dole ta durkusa min". Da gangan ta shirya wannan fitan don tayita gallaza mishi. Tayi shigan larabawa da bakin abaya mai stones tayi kyau sosai. "Abinda yace kenan? Ba karya a ciki, ni son kowa kin wanda ya rasace ai".

Abbas ya iso park yayi parking, ko a jikinta, tayita wayanta. "Hahhhha gaskiyanki wallahi, maza! bazasu san abinda suke rashiba sai sun rasa shi gaba daya". Abbas yanata bubbuga yatsunshi da stirring din mota. "We're here".

"Na fasa, take me to the spa".

"Handsome said to bring you here".

"He said to bring me where ever I want to go", Ta amsa mishi ta koma ga wayarta.

"Hikimat, don Allah! When did that happened? Gaskiya I'll tell my brother, dama sanda wani ya watsama kasa a ido, wani neman hure maka idanun yake".

"Ba sai wanin yayita kayaba, wake bukatan irin wannan nauyin a rayuwarshi". Abbas ya shigo cikin maganarta. Ta dalla mai harara tayi tsaki. "Aikin banza, a bakin mahaukaci aka jin magan..."

Habawa daya fizgi mota a sittin ya harbata gaba a guje ya juyata ta gefe, yana tokyo drift, dama da hagu, can ya taka birki ya tsaya cak. Kuran data tashi ta lafa, ya watso mata kallo mai kaifi. kanta ya dawo tsakanin seat dinshi dana gefenshi. Idanunta sun zaro cikin tsoro, gashin kanta a watse, tuni gyalen ya bar kan. Nishi take sama sama ta kura mai idanu.

"Kashedi, niba abokin wasanki bane, ba kuma bawanki bane da zaki dinga gaya min abinda ranki keso, I won't take that shit from you, don ganin girman yayanki yasa nake raga miki inba hakaba wallahi da sai kinyi regretting ever entering this car. I have sisters like you kuma duk wadda tace zatayimin shagantaka saitata na keyi balleke. Now! kintsa kanki ki zauna kimin shiru, we are going back home."

Jiki a sanyaye da kyar ta mike zaune gashinta ya zubo har zuwa gadon bayanta. kirjinta bugawa yake tayi saboda tsoron ya rabu kashi biyu, tsoron abinda abbas yayi da tsoron abinda abbas zaiyi. Yama akayi ta shiga tsakiyan seats? Tofa, bata taba ganin fushin abbas ba sai yau. Lallai ta taboshi.

Raihana ta gyara zamanta ta jawo gyalenta tayi daga karkashin seat ta yafa akai tana noke kai batason ta hada ido dashi ta mirror. Jikinta sai bari yakeyi har yanzu. "Ko ki kitse gashin nan ko insa scissors in yankeshi". Da sauri ta fara kitse gashinta gama ta natsu, hannayenta kan cinyarta, idanunta kasa.

Abbas ba kanwan lasa bane, baya son raini har dai daga kanwar cikinshi irin wannan. Su ukune maza a wurin mahaifansu, biyu mata. Iyayensu ba masu kudi bane amma basu cikin talauci, madaidaitane. Abbas shine da na biyu, silent killer ne, in kayi mai laifi, toka jira sakamako wanda zaizo maka ta yanda bazakayi tsammaniba.

Duk cikin su abbas ne kawai ya samu aiki me biya in pounds, ya canza musu gida da rayuwa, ya daukakasu a idanun jama'a. Sisters dinshi duk sunyi aure hadda first born dinsu hadi. Abbas ya neman mishi aiki da government yana more rayuwarshi. Mamanshi na alfahari da abbas saboda halin manyanta gareshi.

A da su kashine a danginsu amma sunayin kudi suka tashi daga Gang city suka koma dazzle, ai sai suka zama taurarin family masu fada aji a family din. Abbas ya tsane irin haka shiyasa Inba takai ta kawo ba baya son zuwa gang city. Sai suyita turo mishi 'yan mata, 'ya'yan kannai da yayyin mahaifanshi. Kuraye, wato sunga dallelen yaro yayi arziki bari su turo 'ya'yansu suci. Da sunsha kuruminsu mace dayace ke ranshi kuma ita zai aura, raliya.

Itace mace ta farko data kwanta mai a rai, saboda gaskiyanta da rikon amana. Kyawawan kalamanta masu ratsa zuciya. Ba wadancan makwadaitanba, mayu kawai. Jira yakeyi babanta ya dawo daga forest city inda yake dilan itace yana saidawa a kamfanonin furnitures ko masana'antu.

Ba masu arziki bane asalima raliyace mai ciyarda gidan, don ita kadaice suka haifa. Samun aiki a golden gates ya kawo canjin rayuwa ma gidansu domin handsome yana biya da kyau. Kaman yanda dole kayi mishi aiki da kyau.

Kowane irin gwagwarmayar rayuwa abbas yasanshi kafin ya samu aiki a golden gates, saboda haka bazai tsaya karamar yarinya ta dinga juyashi yanda taga damaba sai kace wani waina.

Ko 'A' bataceba har suka iso villan handsome. Saukanta keda wuya ya hado ta da warning. Ba kullum bane take a tsare, asalima duk bodyguards dinsu shine yayi hiring dinsu, so a karkashin shi suke, kuma umurninshi sukebi.

Ba wani abu bane a wurinshi yasa su kawo mishi ita ya hukuntata a punishment room kuma ko hafiz bazaiga laifinshi ba in ya sanar dashi cewa tayi mishi rashin kunya donko bai tabama handsome karyaba tun haduwarsu, saidaima ya boye gaskiya. Of course bai gaya mata kalamanshi na karshenba.

Punishment room hafiz ne ya ginashi a villanshi don punishing, masu aiki, ko kannanshi da 'yan uwa marasa ji. Dakin yana kunsheda kowane irin tool na horo. Daga dorina, belt, tsumagiyan itace, da wasu abubuwanda baza kayi tunanin za ayi horo dasuba kuma ayi suyi yielding good result. Dokace in aka saka a dakin to sai kayi 24 hours, ba mahalukin da ya isa ya ciroka saika cika wa'adin. Ina ruwan gidan yari. Sukuf sukuf haka ta tafi ya buga motanshi ya tafi. Tun daga lokacin take dari dari dashi.

* * * *

Raihana ta dawo ta zauna. Har yau abin na mata ciwo. Rejection nada kona zuciya wallahi. Wai meyasa abbas baya sontane, ko sha'awarta? Anything dai dagashi. Mutane da dama sun kirata da diva, prettiest, gorgeous, beauty but duk a banza tunda wanda takeyida baya sonyi da ita. Meye aibinta?

Taki ta kwantar da hankalinta ta gane waye abbas, taki ta maida tunaninta akan wace irin mace abbas yake so, taki ta amince da cewa kyaunta bashi ke birge abbas ba, taki ta saukar dakai taga cewa ta hakan zata iya tayi nasara akanshi. Tayaya za ayi ta shiga zuciyan abbas in tana bata mai rai kullum suka hadu da rashin jinta.

Bude hotuna tayi a wayanta tayi scrolling wurin hotonshi inda ta dauka batareda saninshiba, ranar sallah ce yaci shadda maroon tayi mishi kyau sosai donshi yanada haske amma baikai handsome ba. Fuskarshi daga gani tana nuna karkayi wasa dani dinnan koka sani, wanda kesa aji tsoronshi. Giranshi cikakku ya dan hadesu, idanunshi kyar yana kallon wayarta sanda ta daukeshi. Ta tuna a lokacin da sauri ta kaudar da wayar daga kanshi don karya gane ta dauka hotonshi.

Murmushin takaici ya sauka a lebbanta. Ya zatayi ta jawo hankalin abbas kanta? Gayen tauri sai kace giginya, kana fizga kana tauna ga dadi ga wahalan sha. Yanzu ita rayuwarta yana zagaye da wanda baima damu da itaba? Kota mishi maganane? Hm batama mishi magana ba a da amma ya gane manufarta ya tsaidata a lokacin anya bazatayi shiruntaba ta kubuta da sauran mutuncinta?

Ita dai allura cikin ruwace mai rabon kan samu, in rabonshine to zai samu inko ba rabonshi bace hakanan zata hakura dashi. Bayan wannan tunanin, sai taji sakau a ranta. Ta tattara jikinta tabar palon.

Video call sukeyi Asiya na nuna ma hafiz yanda pharmacy din yake ta wayarta. Yayita damunta sai sunyi video call tunda safe shiyasa yanzu dukda darene ta amince tunda ta gama kakkanta wuri. "Nan kuma kicin ne, akwai varieties of foodstuff anan".

"Masha Allah just want to be sure that my baby wouldn't go hungry". Tayi murmushi, idonshi kyar kan dimple dinta. "Haffy kenan".

"Wait, haffy?"

"Baka son sunan?"

"Babe, I love it, da kikace saida naji wani irin sanyi ya ratsa zuciyata. I don't know someone could make me a name I love instantly".

"Glad you love it. Kana gidane?"

"Yeah, wani abokinane yazo so I had to close early".

"He have to mean a lot to you for you to close early".

"Nooo actually, ba wani close friend bane, we met a Washington d.c, wani course ne nayi a NASA, na aerospace".

Asiya ta sauko daga stairs ta zauna gaban kanta, ta bada bayama ma kofar shiga pharmacy din. "Wow,NASA! I love things to do with space, planets, duka"

"Really?"

"Yeah tun ina karama nake sha'awan hakan, nace ma mom tazo muje moon, tace saikin dawo". Suka kwashe da dariya. "Ato haka kawai kija mata bala'i tana zaman zamanta".

"Its interesting though....", ta fara magana hafiz ya katseta.

"Wait, are you alone over there?"

"Yeah, why?"

"Ga wani can behind you". Kirjin Asiya ya bada dammmm, ta sankare a hankali ta juya cikeda tsoro numfashinta sama sama. A waje wani mutumne tsaye yanata kallonta, hada idonsu keda wuya ta rikice. Da sauri ta sauka daga kantan tana jada baya. "Babe, babe listen to me, hide". Asiya ta kalla wayan. "GO NOW!!!"

Habaaa aguje ta haura stairs jikinta nata bari ta shige boss office ta kulle tanata waige waige kaman zatayi kuka. "Asiya look at me, find a place and hide"

"Bu.....but there's no place".

"Shiga bayi ki boye". Da gudu ta shige ta garkame ta ajiye wayan kan sink a tsaye ta rike kai a rikice. Tunda ta makale a wurin babu wanda ya taba zuwa pharmacy din, ko wanda yayi yunkurin shigowa ta gate ya mutu. To waye wannan? Meya keso? Tayaya akayi ya iso bold street, ya akayi bai kamuda cutar ba?

"Babe, listen to me, is there anyone you can call whom is closer to you that can help?"

"Hafiz, we're in an epidemic, no one will come.....".

"Listen, dole akwai wanda zai iya zuwa wurinki ya taimakeki no matter what, don bamu san ko wannan yazo da cuta ba". Idanunta suka zaro cikin tsoro ta taka birki. Tunani yazo mata ta damka wayan hannun biyu jikinta nata rawa.

"Zan kira farouk".

"Is he closer to you?".

"Noo".

"Who else is? Baby please work with me, tell me who is closer to you". A rude take tunanima ta kasayi. "Babe, you should understand that am in no position to help you RIGHT NOW, please think fast".

"Ummiri?"

"Ummi....what?"

"Ummiri, tanada brothers manyane, kuma suna kusa gidansu, she's my friend, she can help".

"Good, call ummi, call your brother, then call me back okay. I'll be waiting, five minutes GO!".

Ringing na biyu ummi ta dauka, a rikice asiya ta sanar da ita halinda take ciki. Ummi ta rude nan take ta shiga action. Farouk na daukan waya Asiya ta rattaba mai halinda take ciki, habawa tuni hankalinshi ya tashi yace mata tayi securing kanta gashi nan zuwa. Ringing daya hafiz ya dauka. Dukda rikicin data shiga amma ta tuna ta mai video call.

"Babe you okay? Kin samesu?"

"Na samu, sunan nan zuwa".

"Shit!!".

"Menene?".

"Kin kulle ko'ina?" Kawai saiji tayi karan bude kofa, da tayi shanya ta manta ta kulle kofan baya da sakata. Kirjinta ya buga, hankalinta yayi sama kaman zata yi kuka. "Ya shigo....".

"Listen babe, please listen keep quiet, okay kar yaji yasan inda kike. I promise to protect you and I will, don't worry, just keep your voice low, zanta miki magana kinji, ki saurara kawai, in situation ya tsananta ki gayamin kinji?"

Ta daga mai kai, ta zauna kan seat din toilet jikinta rawa yakeyi kaman mai jin sanyi. Kyamm ta mike a rikice dataji ana murda hannun kofan boss office, can aka hau dukan kofan. Ta aza hannu a kai hawaye na fita a idonta. "Wayyo Allah na na shiga uku, zai balle ya shigo".

"No babe listen to me, please focus on me, all will be fine babe, Inna lillahi"

Ihu ta kwarma da aka bangaza kofan toilet. "Ahhhhhhhhh" Sai wayan tayi duhu.

A balcony din dakinshi hafiz ya zauna yana video call da Asiya tana nuna mai pharmacy din. Ta gama nuna mishi kicin ta sauka kasan stairs ta zauna a reception suna hira. Sharp idanunshi suka gane mishi mutum a background din Asiya ta wayan.

"Wait, are you alone over there?"

"Yeah, why?"

"Ga wani can behind you". Hafiz na kallon Asiya yaga ta tsorata sosai, a hankali ta juya kanta, ta sauka a rikice tana kallon mutumin. Hafiz yasan dole ya dawo da hankalinta kanshi donya samu tabar wurin. "Babe, babe listen to me, hide". Asiya ta kalla wayan. "GO NOW!!!"

Hafiz ya mike kirjinshi bugawa yakeyi kaman mandiri. Zufa ya gangaro daga goshinshi dukda darene kuma iskan sanyine dashi hardai na gidan saboda shuke shuke.

Tsurama waya idanu hafiz yayi, ya rasa meke mishi dadi, yaushe ya samu macenda ta mamaye zuciyarshi gashi yanzu tana cikin hadari, ba yanda ya iya baya kusada ita balle ya taimaka mata. Abinda kawai zai iyayi shine ya karfafa mata gwiwa.

"Asiya look at me, find a place and hide"

"Bu.....but there's no place". Ta nuna mishi boss office dazu kuma ya tuna ba wurin buya anan, sai kawai tunani yazo mishi.

"Shiga bayi ki boye". Ta shige ta garkame kofan da key. Ta ajiye wayan gaban wani bottle of cream tana kaiwa da komowa cikin tashin hankali. To ai ya kamata ta nema taimakon na kusada ita.

"Babe, listen to me, is there anyone you can call whom is closer to you that can help?"

"Hafiz, we're in an epidemic, no one will come.....". Ya zauna bakin kujeran haki. Yasan da hakan amma ai akwai wadanda suka damu da ita enough zasuzo inta kirasu.

"Listen, dole akwai wanda zai iya zuwa wurinki ya taimakeki don bamu san ko wannan yazo da cuta ba".

"Zan kira farouk". Farouk brother dintane amma gidansu kusa yake?

"Is he closer to you?".

"Noo". Hafiz ya cafka gashin kanshi cikin damuwa. Shi wazai kira yazo ya cece ta a yanzu yanzunnan? Ya tarkata wayan a hannu, kaman ya shiga ya dawo da ita inda yake. Tayi tunani ta gaya mishi da sauri mana.

"Who else is? Baby please work with me tell me who is closer to you". A rude take tunanima ta kasayi. "Babe, you should understand that am in no position to help you RIGHT NOW, please think fast".

"Ummiri?"

"Ummi....what?"

"Ummiri, tanada brothers manyane, kuma suna kusa gidansu, she's my friend, she can help". Ya danji sauki a ranshi, ya goge zufan goshinshi.

"Good, call ummi, call your brother, then call me back okay. I'll be waiting, five minutes GO!".

Wayan hafiz ta Katse daga video call, ya kira abbas. "Meet me now it's urgent". Ya fara neman lambobin mutane daya sani a rose city da zasu taimaka. Wasu sojojine wasu manyan mutane, wasu 'yan majalisu. Amma bold street sun tabbatar mishi imma akwai mutane a ciki, baza a iya fidda suba saboda duk wanda yaje bold street din mutuwa yakeyi kaman annoban nan tazo ta dire tana jiran azo ta kashe. Ya tabbatar musu akwai mutane biyu a Ahmed pharmacy kuma rayuwar daya is in danger su kokarta suga an ceto rayuwarta.

Suka bashi hakuri don gaskiya situation din streets kafin bold street sune abin tsoro, yayiwu na cikin bold street is safe but...hafiz ya Katse wayan. Bata mishi time kawai sukeyi, da a dazzle ne da tuni ya tura alpha team sun cetota.

Alpha team group din bodyguards ne da akama training ta musamman donsu zama best Idan matsala ta ceto ta taso suje suyi aiki. To amma yanzu ya zaiyi? Dole ya dauka hard way don bai shirya rasa asiyanshiba gaskiya. Ya kalla agogonshi minti biyar cip. Wayarshi tayi kara ya dauka video call.

"Babe you okay? Kin samesu?"

"Na samu, sunan nan zuwa". Yaji tace kafin kuma zuciyarshi ta bada damm.

"Shit!!".

"Menene?".

"Kin kulle ko'ina?" Kawai ganin yayi fuskarta ta nuna bala'in tsoro tana kallon gaba da ita, hankalinta yayi sama kaman zata yi kuka. "Ya shigo....". Ai fadin haka keda wuya saiji yayi kaman an watsa mai ruwan sanyi.

"Listen babe, please listen keep quiet, okay kar yaji yasan inda kike. I promise to protect you and I will, don't worry, just keep your voice low, zanta miki magana kinji, ki saurara kawai, in situation ya tsananta ki gayamin kinji?"

Ta daga mai kai yaga jikinta na rawa har kyawawan lebbanta sun dan bude suna rawan tsoro. Yana jin ana buga kofa kaman za a balla. Zuciyarshi harbawa takeyi don baisan me zai faruda asiyanshiba, gashi yana kallo ba halin yin komai. Gani kawai yayi ta aza hannu akai, hawaye suka gangaro kumatunta, idanunta kaman su fadi kasa don ta zarosu.

"Wayyo Allah na, na shiga uku, zai balle ya shigo". Tabdi! Ji yayi kaman ya shiga wayan, ya mike tsaye rikeda wayan, jijiyoyin hannunshi suka bayyana ya kura ma wayan idanu giranshi a hade.

"No babe listen to me, please focus on my voice, all will be fine babe, Inna lillahi. Ya rikice ya rasa abinyi sai kallonta ta wayan.

"Ahhhhhhhhh". Ihu yaji ta kwala. Ai ji yayi kaman an katse mishi jijiyoyin jiki. Ya sankare rikeda waya yanata kallo.

Shigowar abbas balcony ya nufa don yasan by this time hafiz na can. Ya hangoshi ya bashi baya tsaye rikeda wani abu, oh ashe wayace. Yazo ya tsaya gabanshi yanata kallonshi cikeda mamaki don bai taba ganin hafiz ya rudeba. Idanunshi sun fito kwal a zare, bakinshi yadan bude, zufa ya bade goshinshi. Jijiyoyin hannunshi sun fito kwaro kwaro saboda damkan da yayima wayan.

To wai meya sashi cikin hali irin haka? Abbas ya zagayo ta gefen hafiz ya leka wayan yaga duhu. Ya lura video call ne amma baya gani ko jin komai. Ya danja baya ya tsaya gaban hafiz.

"Handsome, I'm here, is everything alright?"

"Get me the hawk".

"Alright, where're we going?"

"I'm going to rose city".

Hawk helicopter dinshice da yasa mata sunan. Helicopter din kaman ta military ce mai gudu kaman jet. In yana bukatan zuwa wani wuri nan da nan, ita yake hawa. Hafiz ya juya ya fara komawa dakinshi abbas yabishi yana magana ta waya. Hafiz ya kalla wayarshi video call din ya dauke.

Suka hau saman villa inda heli pad yake, wato wurin saukan jirgin sama mai saukan ungulu. Hafiz ya lura abbas nata binshi ya taka birki, abbas ya kalleshi. "You stay here and take care of things...."

"No handsome, we go together. Ba abinda zaka gaya min in tsaya anan garin, kafarka kafata, you can't convince me to stay. We go, NOW!" Yayi gaba. Hafiz kawai ya kalleshi cikin mamaki. "Ohwkay". Suna zaune cikin helicopter, pilot na tuki, hafiz da abbas na sanye da ear phones, hafiz sai dunkule hannu yake yana kwancewa, giranshi a hade, hankalinshi a tashe. Jaw muscles dinshi sai clenching sukeyi. Can ya fara motsi da yatsunshi kan cinyanshi. Abbas ya kalla yatsa mai sanyeda zoben azurfa. Ya maida kallonshi ga hafiz.

"Sir, is this the location we are heading to?", direban helicopter ya tambaya.

"That's the coordinates, yes we are heading to rose city", hafiz ya bashi amsa.

"City is in a state of emergency, no fly birds allowed sir", direban ya tabbatar mishi.

"I know, get me as close as you can to the city", hafiz yayi mishi bayani.

Abbas ya lura muryan hafiz yayi kaifi. koma meye ya faru is very serious. Tunda ya kira shi a waya yaji muryarshi ta canza yasan akwai matsala kuma matsalan babbace.

"Handsome, this is too risky, why are we doing this?"

Inma rayuwarshi zata salwantane saidai hakan ya faru amma bazai iya zama baiyi komai ba. Zuciyarshi bazata taba samun natsuwaba, harsai yaje yaga Asiya cikin koshin lafiya. Inko an mata illah, to wanna mutumin ko karshen duniya yaje, saiya je ya jawoshi ya masa azaba mai tsanani dazai gwammace gwara mutuwarshi.

"Because she's in danger". To wacece in danger? Tunani yazo mishi, rose city? Ya kallo hafiz da sauri. "Asiya? She's in danger? How?"

"Wani dan iskane yazo yayi attacking dinta inda take, I hope she's fine, nasata ta kira kaninta da wata friend dinta with her brothers, to help her at that time, hope they made it there". Ya duba wayarshi dake zaune a cinyarshi, ya kara kira, switch off".

"Ow".

"What?" Hafiz ya wurgeshi da kallo.

"Oh I thought.... CD ne ya kamata".

"What!!!"

"You said she's in danger...".

"What the hell are you talking about! Me kake cewane!! Yama za ayi kace haka!!! Have you gone mad.....". Hafiz ya balbale shi.

"Allah huci zuciyarka, ba haka nake nufiba". Dakika daya shiru, dakika biyu shiru, saida aka kwashe dakikai goma basuce komaiba, abbas ya kalla hafiz ta gefen ido. "I'm sorry handsome, I hope tana lafiya, kuma karka damu insha Allah tana nan kalau". Wayan hafiz tayi kara da gudu ya dauka, video call ne.

"Honey is that you? Sweetheart are you okay?"

"Haffy, I'm good". Muryarta a mace.

"What happened? Call din ya katse, I couldn't reach you for the pass 1 hour"

Bakinta ya bushe, idanunta sunyi kaman tana jin bacci. "I had a flat battery, I just finish charging shine na kiraka. Nasan hankalinka zai tashi. Everything is fine now".

Everything is fine a ina? Yanaso ya shake wanda ya bata tsoro. "Waye wannan wawan daya baki tsoro?" Ta danyi murmushi.

"Wani me kwasan gawane, sunanshi Usman. Yace duka mutanen headquarters dinsu sun mutu. Shine ya dawo gida, abinci ya kare. Neman abincinne ya kawoshi har nan, yace kwananshi uku bai ciba".

"Shine yazo ya tsorataki?"

"Shima yaji tsoro....."

"Tsoro! Nuna min shi inga waye wannan". Tana 'yar dariya ta nuna mishi Usman, se tula abinci yakeyi a baki.

"Oga....", usman yace baki cikeda abinci.

"Wato Kaine ka kusa kashe min mata?"

"Ah haba....".

"Ni kuma ka kusa samun heart attack".

"Hah oga afuwa nake nema". Asiya tayi dariya har dimples dinta suka lotsa, hafiz nata kallonta cikeda kauna. "Kai haffy".

* * * *

Dole tasa Usman fitowa daga gida saboda yunwa ta addabeshi, ya cinye duk abinda ya tanada babu komai ga yunwa kaman ta kashe shi. Yayita tafiya yanabi unguwa unguwa kozaiga dan shago amma inaaa duk inda yabi babu shago, daga baya ya lurada sojoji masu yawo tareda likitocin. In suka Kama mutane masu yawo harbesu sukeyi, sai likitocin su ja jininsu susa jinin a wata akwati su tafi abinsu.

Bayan 'yan awanni sai yaga wadanda aka harbe sun tashi kaman dama bacci sukayi. Abin yakai har kutsa kai sukeyi cikin gidan mutane suna harbesu saisu ja jini. ko shima Usman da kyar yasha da wani soja ya sashi gaba, yayi gudu harna Inna naha sai yaga kaman zai kubuce sai sojan ya bullo mishi.

Zuwanshi greenfield road wanda ke kusa da layinda ba a shiga, bold street, shine ya kubuce ma wannan sojan. Yaci wuya kwana kusan uku a jere baici komai ba sai ruwa ko shima ruwan da kyar yake samu.

Duhu ya riga yayi lokacinda hasken fitilan signboard din ahmed pharmacy ya dallo idanunshi. Kai tsaye ya wuce zuwa gate yaga ansa kwado an datse. Haurawa yayi ya shiga wurin, yaga an rufe kofar shiga cikin wurin shima da kwado amma kuma kaman yana hango wata ta glass tana zaune kan kanta ta bashi baya.

Juyowanta keda wuya ta rikice tana sonta gudu. Usman yayi iya kokarin yayi mata magana amma makoshinshi ya bala'in bushewa. Can yaga ta balla da gudu ta haye sama. Ya rasa ya zaiyi saiya fara zagaya wurin kozaiga wata kofa. Cikin sa'a yaga karamar kofa ta baya yana budeta ko ta budu ya shigo.

Wurin tsaf yake fari fet. Yazo wurin reception ya shiga inda magunguna suke yana neman ruwa babu, sai yabi hanyan stairs ya kalla sama ya haura. Isansa saman keda wuya yaji surutu daga nesa nesa, ya nufa hanyan boss office, kila yarinyan nada ruwa. Hadiye yawu yayi don ya iya mata magana karta kara tsorata.

Handle din boss office ya ja amma yaki budewa kaman an kulle. Toba nan yaji muryartaba? Meyasa ta rufe? Yayita ja har haushi ya kamashi ya bangaza kofan ta bude ya shigo yaga ba kowa. Ruwa kawai kwalkwaluwarshi ke aiyana mishi. Ya kallo kofan bayi, yawwa ko banza zai samu ruwa a pampo yasha.

Taba kofan da zaiyi yaji itama a kulle, haushi ya kara kamashi, wai anan komai kullewa sukeyi? Ya fara bangaza kofan, tun yanayi a hankali harya fara yi da karfi. Yasa karfinshi na karshe ya bangazata da karfi. Kawai yana murnan zaisha ruwa wata mahaukaciya tayi ihu tayi cikinshi ta nausheshi a ciki, ya fadi ta tsallakeshi ta gudu.

Ganinshi kawai yayi warwas a kasa, ya rasa ya akayi hakan ta faru. Mikewa yayi da sauri ya ruga wurin pampo yasha ruwa kaman ba gobe. Sannan ya fito daga bayin yana gyaran murya.

"Baiwar Allah don Allah kiyi hakuri, kishine nakeji na kasa magana. Ina kike? Don Allah ki fito ba abinda zan miki wallahi".

"To meyasa ka shigo da karfin tsaya?!"

"Kishine wallahi, tun safe nake neman ruwa ban samuba sai yanzu. Banci komai ba tun kwana ukun da suka wuce, don Allah in akwai abinci ki taimakamin dashi don Allah".

Asiya ta fito daga bayan curtain rikeda wuka, tanata kallonshi, a firgice yake, kayan jikinshi sunyi datti kamanme, gashi kakkarfane. Ta kwantarda hankalinta tanata nuna mishi wukan. "Abinci kakeso?! Amma ni kakusa halakani! Aiko tsoron karan kanshi ya isa ya halaka mutum".

"Don Allah kinyi hakuri, wallahi banzoda cutaba. Yunwace, ba kamanma kishi".

"Yanzu bakajin kishinne?".

"Nasha ruwa a bayi ai".

"I'm safe kenan"

"Hahhh ayi hakuri". Ta sauke wukan kasa.

"Muje kicin inga abinda zan samoma, tayaya ma akeyi kazo nan?" Suna tafiya yana mata bayani yanda akayi yazo. Suka isa kicin inda ta dumama mishi jollof ta bashi juice da ruwa.

Taje toilet ta dauka wayarta, ta tattaba amma bata kawo wutaba ta dauka charger ta dawo kicín tasa, bayan tadanyi charging ta kunna, lafiya lau ta fara kiran hafiz.

"Um bari in kira hafiz nasan yana can hankalinshi a tashe".

* * * *

"Oh watoma harda girki kike masa". Ta kara murmusawa. "Ai akwai kawai dumamawa nayi na bashi, kwana uku fah baici komaiba".

"Um lallai kin kyauta. I feel like it is my fault wannan rudanin da kika shiga".

"I feel like laifinane, nayi attacking poor man din, but akwai kamshin gaskiya a maganarka, laifinkane. Ya za ayi ka bani tsoro hakanan".

"I'm so sorry baby, forgive haffy dinki, pleeeease".

"Ya wuce ai, tunda yanzu na zama matarka".

"Ai dama dana ganki babe, ban daukeki a matsyin wata budurwataba, matatace kawai". Wani gishirin dadi ya barbade zuciyarta.

"A ina kake yanzu?"

"Um.....hanyan zuwa rose city".

Don Allah don darajan annabi da iyayenshi, haka Asiya tayita rokonshi da karyazo. Gari ba lafiya amma mutum ya dage saiyazo, so yake ya mutu kafin su hadu? Ya tabbatar mata da cewa a yanzu haka da take magana dashi yana border din rose.

Akwai rudu a halinda ta shiga amma komai ya warware da kanshi, meye na wahalan zuwa kuma. Hafiz ya bata hakuri yace yayi setting GPRS zaizo nan da 24 minutes. What!!! Bazai hakura ba kenan. Amma taya za ayi ya shigo garinda aka rufe, kosu na ciki basu fita. Sannan ma baya tsoron cutar nanne, idanshi bai tsoron ta kamashi, baya tsoron yazo ya bada mata, inbai mutuba kafin ya iso?

Oho ita ta sani yanda yazo dole saiya shigo, kuma zai kare kanshi karta damu. Babban burinshi ya hadu da ita, itama tanada burin haduwa dashi amma ba irin hakaba, cikeda fargaba. Yace ta mishi addu'a gashi nan shigowa.